Ƙungiyar Ɗalibai ta NAIMSS Reshen Jami’ar Bayero Kano ta Karrama Auwal Barde

0
180

Kungiyar Daliban Sashin Koyar da Ilimin bayanai da Kafafen Yada Labarai ta Kasa reshen Jami’ar Bayero dake Kano ta Karrama wani fitaccen Dan Siyasa kuma Dan Kasuwa, Alhaji Auwalu Barde bisa jajircewarsa wajen tallafawa matasa da dalibai.

A yayin da yake jawabi a madadin shugaban kungiyar, Yusuf Sani Maitama ya bayyana cewa sun karamma Honorable Auwal Barde ne bisa jajircewarsa wajen tallafawa al’umma da kuma inganta rayuwar matasa.

Shugaban Daliban ya ce sun bincika sosai sun gano cewa, Auwal Barde na daga cikin yan siyasar dake tallafawa Dalibai.

Anasa Jawabin, Honourable Auwalu Barde ya bayyana godiyarsa ga daliban bisa zaben da suka yi masa a matsayin wanda suka karrama.

Sannan ya hore su da su tsaya kan karatunsu da ci gaba da dogaro da kansu.

Haka kuma ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa kungiyar a kowanne mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here