Ranar Ruwa ta Duniya: Rabon da Mu Samu Ruwan Fanfo Mun fi Shekara 10 -Mazauna Kurna

0
139

 

A yayin da ake bikin Ranar Ruwa ta Duniya a 22 ga watan Maris na kowacce shekara kamar yadda majalisar dinkin Duniya ta ware, Jaridar PRIME TIME NEWS ta zagaya wasu unguwannin dake cikin birnin Kano inda muka tattauna da wasu mazauna unguwannin kan yadda suke fuskantar matsalar ruwan sha tsawon shekaru.

Mazauna Unguwannin Kabara, Soron Dinki, Makwarari, Kwanar Goda, Gabari, Agadasawa sun shaidawa Jaridar PRIME TIME NEWS cewa sun shafe tsawon shekaru rabon da su samu ruwan fanfo.

Wani Magidanci da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, “Kullum cikin dare muke fitowa muna jiran a kawo wuta mu samu ruwan burtsatsai, rayuwarmu tana cikin hatsari saboda baka san me zai faru da kai cikin dare ba.

“Ya’yanmu suna rasa samun isasshen bacci wani lokacin ma har makara suke yi a makaranta saboda karancin ruwan sha da muke fuskanta”.

Shi ma wani Saurayi Mazaunin Unguwar Kurna ya ce a duk Wata yana kashe kudi fiye da dubu 10 wajen siyawa gidansu ruwan Jarka

“Ina Kashe kudi sama da dubu 10 wajen siyan ruwa a gidanmu, mun fi shekara 10 bamu da ruwa a Kurna.

“Ina da fili a Kurna amma na fara tunanin siyar dashi saboda matsalar ruwa bazan so zama a inda ba ruwa ba”.

 

Mun yi yunkurin jin ta bakin hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano amma abun ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here