EFCC za ta binciki duk wani ɗan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsa a Shafukan Sada Zumunta

0
474

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, mataimakiya ga shugaban Najeriya kan kafofin sada zumunta, Laurette Onochie, ta ce hukumomin da ke yaƙar rashawa wato EFCC da ICPC za su binciki ƴan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsu musamman a shafukan sada zumunta.

Ms Onochie ta shaida hakan ne a shafinta na Twitter ranar Litinin, tana mai cewa za a gayyaci irin wadanan mutane domin bincike kan yaɗa suka mallaki kadarorin da arzikin da suke nunawa.

Onochie ta ce, “binciker yadda mutum ya ke rayuwarsa za ta kasance wajibi a Najeriya bisa sharuɗa na doka”.

Wannan na zuwa ne bayan a makon da ya gabata, shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya fitar da sanarwa cewa wajibi ne duk wani ma’aikacin banki ya bayyana kadarorin da ya mallaka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here