Dalilan Da yasa PDP Ke Shirin Tsayar da Ɗan Arewa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

0
422

Rahotanni na na bayyana cewa Jam’iyyar PDP na shirin tsayar da Dan takarar Shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2023 daga Arewa.

Hakan na zuwa ne bayan da rahotan da kwamitin da jam’iyyar ta kafa don bibiyar dalilan da yasa ta sha kashi a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 ya bada shawarar yadda jam’iyyar za ta dawo Mulki.

Kwamitin mai mambobi 14 karkashin shugabancin Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi, ya bada shawarar dena amfani da tsarin karba-karba.

Wani Jigo a jam’iyyar kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar ya shaidawa jaridar Daily Independent cewa za su amfani da shawarwarin kwamitin inda ya ce manyan kusoshin jam’iyyar nason a mika tikitin takarar shugaban kasa ga yankin Arewa.

Ya ce zai zama ba adalci jam’iyyar ta kara bawa yankin Kudu dama kasancewar yankin ya shafe tsawon shekaru 13 a shekaru 16 da PDP tayi tana mulki.

“Kwamiti sun gama aikinsu yanzu ya rage ga masu ruwa da tsaki wajen duba shawarwarin da suka bayar amma ina tabbatar maka za’a dau shawarar dake cikin rahotan.”

Shima wani jigo a Jam’iyyar ya bayyana cewa matukar jam’iyyar na son lashe zaben shekarar 2023 tilas ta tsayar da tankara daga Arewa.

Haka nan anjiyo Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a tattaunawa da BBC yana fadin cewa a shirye yake ya goyi bayan dan takarar jam’iyyar PDP da zai fito daga Arewa matukar hakan zai sa jam’iyyar ta samu Nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here