“Ban Gudu Daga Najeriya ba” -Salihu Tanko Yakasai

0
87

 

Tsohon Hadimin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai ya musanta rahotan dake cewa ya gudu ya bar Najeriya.

Salihu Tanko Yakasai wanda ya rasa gujerarsa bayan sukar gwamnatin APC kan batun tabarbarewar matsalar tsaro ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook.

“Na yi posting cewa zan tafiya, bayan na isa inda zani yanzu, na kunna waya na ga ko ina a harabar social media harda manyan jaridun kasar nan ya cika da labarin cewa wai na gudu daga kasar, wannan ba gaskiya bane kuma babu ma a inda maganar nan ta samu tushe. Hutu na je kuma zan dawo gida In Sha Allah, dan bana jin da wanda ya kai ni san zama a Kano, Abuja ma na kasa komawa da zama bare na bar kasar gaba daya.

“Wannan ta sa dole manyan mu a bangaren aikin jarida da malamai na koyar da aikin jarida su yi nazari akan labarai irin wannan marasa tushe. Na farko dai a dinga bincike kafin ayi labari irin wannan mara hujja, da sun tambayi yan’uwa na ko aminai na, da zasu san hutu na tafi, ko kuma suyi hakuri idan na isa su tambaye ni na fada musu da kai na, kuma duk wanda ya sanni dama ya san ina da shaawar zagaya duniya. Kawo yanzu na je kasashe 46, kuma buri na ne naje kusan duk manyan kasashen duniya, amma yawon bude ido ba komawa can da zama ba.

“Dan haka nake kira da a kalli aikin nan kafin ya lalace gaba daya, a dinga tsawatar wa da duk wani dan jarida da yayi labari irin haka bada hujja mai kwari ba, domin yana zubar wa da gidajen jaridun kima, sannan kuma yana kawo shakku akan wasu labari da zasu buga a gaba.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here