“Za’a Ga Gawarwakin Masu Daukar Nauyin Yan Bindiga a Jihar Zamfara Idan har…..” – Gwamna Matawalle

0
275

Gwamman jihar Zamfara, Bello Matawalle ya rantse da Al-Qur’ani mai girma cewa bashi da alaka da yan bindigar dake addabar jihar.

Sannan ya kalubalanci mazauna jihar kowannensu ya rantse da Al’Qur’ani kan cewa basu da hannu a matsalar tsaron da ta zamewa jihar Kadangaran bakin tulu.

Gwamman ya yi kalubalen ne a yau Lahadi a Birnin Gusau yayin da yake karbar lambar girmama a matsayin Khadimul Qur’an da Cibiyar Makaranta Qur’ani ta bashi.

“Kamar yadda na fada, batun matsalar tsaro ba wai kawai na Gwamnatin tarayya, gwamna da sauran jami’an tsaro bane; batun matsalar tsaro abu ne da ya shafi kowannenmu, kar musa siyasa cikin lamarin tsaro.

“Na rantse da Al’Qur’ani mai girma cewa idan nasan ko kuma ina daga ciki ko nasan wanda ke hada wannan ta’addancin, ko da hannuna aciki ko wani daga iyalina, Allah Kar ya bani abin da nema a wanann rayuwa” inji shi.

Gwammna Matawalle ya kara da cewa, Ina kalubalantar dukkan mutanen Zamfara tun daga babanmu, Aliyu Gusau zuwa Yarima Bakura da dukkan mukarraban gwamnati da sauran yan siyasa su yi irin wannan rantsuwar”.

Gwamnan ya ce idan har aka yi wannan tsinuwar tabbas za’a ga gawarwakin masu daukar nauyin yan Bindiga a jihar Zamara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here