Ɗan Najeriya Kelechi Iheanacho ya taimakawa Leicester wajen doke Manchester United

0
144

Daga Junaid Idris Gezawa

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, Leicester City ta kai zagayen dab da ƙarshe a gasar FA a karon farko tun kakar 1981-82 bayan ta fitar Manchester United a King Power da ci 3-1

Yanzu Leicester za ta haɗu ne da Southampton a Wembley a zagayen dab da ƙarshe.

Ɗan Najeriya Kelechi Iheanacho ne ya taimakawa Leicester doke Manchester United.

A ranakun 17 da 18 za a yi fafatawar zagayen dab da ƙarshe a Wembley yayin da kuma za a buga wasan ƙarshe a ranar 15 ga Mayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here