Tsofaffin Daliban Da Sukayi Karatu A Amurka Sun Horar Da Masu Bukata Ta Musamman Sana’o’i A Kano

0
126

 

Kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Kano da sukayi karatu a kasar Amurka ta horar da mutane masu bukata ta musamman sana’ar dinki da kuma walda a jihar Kano domin karfafa musu gwiwa akan dogaro da kansu.

Kungiyar ta Kennedy Lugger Youth Exchange and Study wadda take da reshen ta na Youth Alumni Association of Nigeria ta horar da masu bukatar ta musamman ne a ofishinsu dake kan titin jami’ar Yusuf Maitama Sule University dake Kano.

A jawabinta Prof. Gaji Fatima Dantata, taja hankalin matasan akan cewa kada suyi kasa a gwiwa wajen tallafawa masu bukata ta musamman idan kuma tayi kira ga wna suka ci gajiyar shirin akan suyi amfani da horon da suka samu domin bunkasa sana’ar da aka koya musu.

Fatima Umar, wadda day ace daga cikin wadanda suka je kasar Amurka sukayi karatu ta bayyana yadda suka fara aikin sannan kuma ta bayyana cewa sun zabi masu bukata ta muamman ne domin sune suke bukatar taimako sannan suna zuwa asibiti da gidan marayu da wasu wuraren daban.

Mataimakin Darakta na bibiya da tantance inganci na sashin tsare-tsare da kididdiga na ma’aikatar ilimi ta jiha, Shehu Abbas Na’Abba ya bayyana farin cikinsa ga wadannan matasa sannan kuma ya ce hakan ya nuna jajircewar hukumar ilimi ta jiha wajen ganin an samu ingantaccen ilimi a jiha.

An dai koyar da mutane 10 mata dinkin keke sannan an koyar da maza aikin walda sannan kuma an basu kayayyakin da zasu ci gaba da aikin bayan an kammala basu horon ya yinda suka nuna farin cikinsu ga wannan tallafi da suka samu

Kayayyakin da aka koyawa masu bukata ta musamman RR

Su ma shugabannin kungiyoyin masu bukata ta musamman na jihar Kano da suka halarci wajen sun bayyana farin cikinsu kan yadda tsoffin daliban suka zabi masu bukata ta musamman domin koya musu sana’a tare da basu tallafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here