Bidiyon cusa Daloli a Aljihun Babbar Riga na Karya ne – Ganduje

0
321

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce Bidiyon da aka ganshi yana karbar daloli yana sawa aljihu na karya ne.

Jaridar Daily Nigerian dai ce ta fitar da bidiyon wanda ya yadu sosai a shafukan sadarwa na zamani.

A wani shiri na sashin Hausa na BBC mai suna ‘A Fada A Cika’ wanda gidauniyar MacArthur ke daukar nauyi, Ganduje ya ce Bidiyon na karya kuma kwanan nan wadanda suka hada shi zasu ji Kunya”.

 

“Wannan Bidiyo Karya ne , muna shirin tabbatar da hakan, bana so in fada abinda muke yi, amma ina tabbatar maka cewa wadanda ke da hannu wajen fitar da bidiyon za su ji kunya, inji Ganduje.

A halin yanzu Ganduje yana kotu yana kalubalantar mawallafin jaridar Daily Nigerian Jafar Jafar akan bidiyon da ake zargin an dauka a shekarar 2017, kafin fitar dashi a 2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here