2023: ”Ba zan Goyi Bayan Takarar Jonathan Ba” -Gwamna Wike

0
94
Gwamnan Jihar Rivers,

Daga Junaid Idris Gezawa

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce bazai goyi bayan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ba koda kuwa ya samu damar yin takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 karkashin tutar jam’iyyar APC.

Yayin da yake zantawa da Sashin Pidgin na BBC a birnin Fatakwal, gwamman ya ce ta sanadinsa ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya zama gwamman Rivers.

Wike ya ce ko Jonathan ya san cewa Wike zai yake shi idan ya shiga Jam’iyyar APC Kuma ya samu tikitin yin takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Ya ce: “Ni dan jam’iyyar PDP ne, Idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu tikitin takara a jam’iyyata, zan goyi bayansa bazan yi anti-party ba. Idan ya samu tikitin takara a APC, bazan goyi bayansa ba saboda bazan yi Anti-party.

“Ya sani bazan goyi bayansa ba a APC ko shi dan Kudu ne. Bana irin wannan siyasar muna magana ne a kan jam’iyya”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here