Shafukan Facebook, Instagram da WhatsApp Sun Katse a Fadin Duniya

0
109

Shafukan Facebook da Instagram da WhatsApp sun dauke na tsawon Sa’a daya a fadin Duniya wanda hakan ya haifar da damuwa ga masu amfani da shafukan sadarwar na zamni.

Shafukan wadanda dukkansu mallakar Kamfanin facebook ne sun katse ne a yau Juma’a da misalin karfe 5:30 agogon GMT karfe 6:30 a gogon Najeriya.

Masu ziyartar shafun Instagram an nuna musu cewa shafin bazai budu ba(‘5xx Server Error’, ba tare da karin wani bayani ba.

Haka abin yake ma a shafun Facebook inda mutane da dama suka kasa samun damar shiga shafin.

Masu amfani da shafukan sun nuna matukar fushi kan yadda suka gaza samun tattaunawa da abokansu da iyalansu da abokan aiki ta shafukan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here