Hisbah ta kama Mutane 30 da ake Zargin Suna Siyar da Naman Kare da Burkutu a Kano

0
108

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama mutane 30 dake siyar da naman kare, da giyar da ake hadawa a gida wacce aka fi sani da Burkutu.

Yayin da yake yiwa manema labarai jawabin kan kamen, Kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano, Haroun Ibn Sina, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Lahadi a Agangara, dake Badawa a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

A cewarsa, Kamen ya biyo bayan korafe-korafen da al’ummar yankin ke yi.

Ya ce bayan gudanar da bincike, hukumar ta gano cewa ana siyar da wadandan abubuwan a bainar jama’a a wajen.

“Wannan ba abinda za’a lamunta bane a jihar Kano”, Inji Malam Ibn-Sina.

Ya ce: ” Aikin hadin gwiwa ne aka yi a Agangara dake Badawa a yankin karamar hukumar Nassarawa.

“An kai sumamen ne bayan samun korafe-korafe daga mazauna yankin inda suka ce yankin na barazana ga zaman lafiyar yankin”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here