Allurar Rigakafin Korona bata da wata Illa a jikin Mutum – Dakta Sufi

0
184

Dr. Musa Abdullahi Sufi mai kula da kungiyoyin da suka shafi kiwon lafiya da gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo ya bayyana cewa allurar rigakafin Korona ba ta da wata illa ga lafiyar mutum sai dai ta zama kariya daga kamuwa daga cutar.

Dakta Sufi ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai bayan da aka yi masa allurar rigakafin a Kano.

Sufi ya ce daman wasu daga cikin jama’a basu fiye amincewa da wani sabon abu da yazo ba.

“Duk Wani Abu da Zai zo mana, indai sabo ne bamu san shi ba ko Boko da tazo mana sai dai aka dinga ja baya da ita ana zargin cewa za’a dauke mutane daga addininsu za’a sauya musu rayuwa .

Dalilan da yasa ake samun zarge-zarge kan wannan abu na farko shi ne siyasar Duniya da kuma siyasa ta tsakankaninmu , siyasar duniya shi ne duk lokacin da wasu ke ganin wasu zasu yi nasara kan wani abu za su yi kokarin yadda zasu yake su”.

 

Ya kara da cewa wasu na fadin zarge-zargen cewa Korona Karya ce saboda son rai ko domin samun suna sakamakon hakanne wasu mutanen ke nuna shakku kan cutar.

“Idan zamu iya tunawa lokacin da Korona ta zo cewa aka dinga yi bata yiwa yan Afrika Illah amma idan ka duba, bakaken fata a Kasar Amurka sun fi mutuwa daga cutar.”

Dangane da samun rigakafin cikin kankanin lokaci kuwa, Dakta Sufi ya ce a kullum duniya na samun ci gaba shi yasa aka samun rigakafin kasa da shekaru daya.

“Misali da a jaki ake zuwa aikin hajji, amma yanzu a jirgi ake zuwa a chan baya idan aka ce cikin a wanni uku zaka je ay baza ka yarda ba”.

Haka kuma Dakta Sufi ya yi bayanin cewa, saboda jama’a su amince da ingancin allurar yasa aka fara yiwa shugabbanni a matakin farko da kuma ma’aikatan lafiya.

Sannan ya yi kira da al’umma da su tabbata sun je anyi musu allurar rigakafin tun da wuri domin kuwa nan gaba zata iya yuwuwa sai mutum ya biya kudi za ayi masa.

Daga karshe ya yabawa gwamnatin jihar Kano, da gwamnatin Kano kan yadda ake aikin wayar da kan al’umma domin suje ayi musu rigakafin na Korona

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here