Yanzu-Yanzu: Kotu ta bada Belin Mahdi Shehu

0
167

Babban kotun tarayya dake zamanta a Kano ta bada belin Mahdi Shehu wanda ya musanta zarge-zarge shi da gwamnatin jihar Katsina ke yi masa.

An bada belinsa ne kan kudi Naira Miliyan 10 da kuma kawo mutum guda da zai tsaya masa. Kotun ta ce wanda zai tsaya masa dole ne ya zama mazaunin Kano da yake da gida a Kano.

An dage shari’ar zuwa 19 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraran karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here