Cutar Amai da Fitsarin Jini ta Ɓulla a Ƙauyen Gwangwan dake Jihar Kano

0
163

Mazauna Kauyen Gwangwan dake karamar hukumar Rogo ta jihar Kano na fuskantar barkewar sabuwar cuta yayin da wadanda cutar ta kama ke yin amai da fitsarin jini.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa wurare shida a kauyen cutar ta shiga yayin da mutane 56 suka kamu da cutar tun bayan barkewarta.

“Unguwar da cutar ta yadu sun hada da Unguwan Rijiyar Dadi, Gwanwan Gabas, Gwangwan Yamma, Unguwar Tsarmai, Gangare da unguwar Kofar Fada.

“Mun kai kusan mutane 30 zuwa babban Asibitin Rogo a rana guda da bullar cutar.

” Mutum daya ne ya rasa ransa sakamakon bullar cutar. Mutanen da suka kamu da cutar na korafin kashe kudaden da suka yi kan cutar”, inji majiyar.

Kauyen Gwangwan, wanda ke da nisan Kilo Mita 136 daga birnin Kano kuma yake a karamar hukumar Rogo yana cikin yanayi na ban tsoro, inda mutane ke nuna damuwa kan cutar.

Wani mahaifin yara biyu da suka kamu da cutar ya yi korafin cewa ya kashe kudi sama da Dubu 20 a Asibiti don ganin yaran sun samu lafiya duk da matsin tattalin arziki da ake ciki.

Wani magidanci wanda mutane takwas suka kamu da cutar a gidansa ya ce ya shiga matukar damuwa.

Wasu daga cikin iyalansa da suka kamu da cutar wadanda suka hada da matarsa da mahaifiyarsa da ya’yansa basa iya tsayuwa sakamakon illar da cutar ta yi musu.

Ya yi korafin cewa, ya kashe kudi kusan Naira Dubu Dari tsakanin Asibitin Rogo da na Gwarzo kuma ba tare da samun sakamako mai kyau ba.

Wani ma’aikaci a karamin asibitin garin, ya ce cutar bata daga cikin wacce za su iya da ita shi yasa mutane ke tururuwa a asibitin Rogo.

Haka kuma, Wata majiya a Asibitin na Rogo sun shaida cewa ba su da masaniya kan bullar wata cuta.

Haka kuma, mahukunta a ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano sun ce ma’aikatar ta samu labarin bullar cutar sai dai mutane 4 ne kadai suka kamu kuma an basu magani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here