A Dukkan Mutane 7 na Yan Najeriya Ana Samun Mutum 1 dake Ta’ammali da Muggan Kwayoyi -NDLEA

0
87

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa, ya ce ana samun mutum daya a cikin mutane bakwai na dukkan yan Najeriya wanda ke ta’ammali da muggan kwayoyi.

Buba Marwa ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a gidan gwamnatin jihar dake Marina, ranar Laraba.

Marwa dai tsohon gwamnan jihar Legas ne a mulkin Soja.

Shugaban Hukumar ta NDLEA wanda ya jinjinawa kokarin gwamnatin Sanwo-Olu wajen magance shan miyagun kwayoyi ya yi kira da a dinga yiwa dalibai da yan siya gwajin shan miyagun kwayoyi.

Marwa ya ce bai kamata dalibai da ’yan siyasa masu rike da mukami da masu neman mukamai na mulki su kasance wadanda muggan kwayoyi su ka daskare wa kwakwalwa ba.

 

Sannan ya kara jaddada wa gwamnan cewa akalla akwai mutum milyan 4.5 masu tu’ammali da kwaya da Jihar Lagos kadai.

A ziyarar wadda ya kai ta kwanaki uku, Marwa ya umarci zaratan jami’an NDLEA na Lagos su tabbatar sun kakkabe jihar daga muggan ’yan kwaya da sauran masu tu’ammali da ita, kama daga sayarwa, safarar ta da jigilar ta.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here