Ƙungiyar malamai Ta nemi Ganduje ya cire Haramcin wa’azi kan Abduljabbar

0
248

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, majalisar malaman Musulunci ta ƙasa a Najeriya, Nigeria Council of Ulama, ta yi kira ga Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ɗage haramcin yin wa’azi kan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara tare da buɗe makaranta da masallacinsa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito muƙaddashin shugaban majalisar, Sheikh Dan’azumi Tafawa Balewa, yana magana da manema labarai a garin Bauchi a yau Alhamis, inda ya ce majalisar ta damu da haramcin da aka yi wa malamin.

Ya ce bisa damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa na yin addinin da yake so da kuma adalci, ya kamata Ganduje ya ƙyale Abduljabbar ya ci gaba da wa’azi.

“Wannan ‘yanci da kundin tsarin mulki ya bayar ya yi daidai da koyarwar Alƙur’ani mai tsarki a wajen da Allah ya ce ‘Babu tilastawa a addini,” in ji malamin.

“Muna girmama ra’ayoyin mutane mabambanta kuma burinmu shi ne mu yi tayin tattaunawa da fahimta tsakanin Musulmai masu mabambantan ra’ayoyi.

“Muna roƙon mai girma gwamna kuma ƙwararren ɗan siyasa wanda muke girmamawa da ya sake duba matakin kuma ya ɗabbaƙa koyarwar Alƙur’ani irin yadda Allah Ya umarci shugabanni irinsa su yi adalci ta hanyar bai wa kowa dama iri ɗaya.”

A watan kwanakin baya ne Gwamna Ganduje ya hana Abduljabbar gudanar da wa’azi tare da yi masa ɗaurin talala a gidansa bayan an zarge shi da yin kalaman da za su iya tayar da fitina a cikin wa’azin nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here