Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasar Tanzania John Magafuli Ya Mutu

0
91

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, shugaban Tanzania John Magafuli ya mutu. Mataimakin Shugaban ƙasar Samia Suluhu ne ya tabbatar da mutuwar shugaban cikin wata sanarwa da aka sanar a kafar yaɗa labaran ƙasar.

A cewar mataimakin shugaban, Mista Magafuli ya mutu ne da yammacin ranar Laraba a asibitin Mzena da ke Dar es Salaam sakamakon ciwon zuciya.

Ya shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar. Saluhu ya ƙara da cewa a ranar 14 ga watan Maris ne jikin shugaban ya yi tsanani inda kuma aka kwantar da shi a asibiti – a nan kuma ya mutu.

Ya mutu ne yana da shekara 61 da haihuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here