Wasu Daga Cikin Manyan Mawakan Hip-hop basa Jan Ƙananan Mawaƙa a Jiki – Mawaƙi Mome Neh

0
302

 

Daga Junaid Idris Gezawa

Mohammad Umar Usman Wani Mawakin Saurayi ne mai tasowa, a tattaunawar da ya yi da wakilin jaridar PRIME TIME NEWS, Junaid Idris Gezawa , ya bayyana yadda ya tsinci kansa a fannin waka.

Ga Yadda Tattaunawar ta Kasance:

PRIME TIME NEWS: Mene ne cikakken sunanka?

•Mohammad Umar Usman.

PRIME TIME NEWS: Mutane suna kiranka da inkiyar Mome neh. Mene asalin sunan?.

•Wato abinda yasa ake kirana da Mome Neh Shi ne Missali, Da Larabci Muhammad Da Hausa Mohammed Da Kanuri Modu Toh Kaga Da Turanci kuma Mome.

PRIME TIME NEWS: Kafin mu tabo fannin Sana’arka ta waka. Mene takaitaccen tarihinka da mai karatu zaiso ya karanta?.

•Eh Toh Ni Sunana *Mome Neh* Kamar Yadda kukafi Sani, Ni mazaunin garin Maiduguri Ne Jahar Borno, Anguwan Ngomari Airport, Ina Karatu a makarantar Kashim Ibrahim college Of Maiduguri Dake cikin garin Maiduguri.

PRIME TIME NEWS: Kai tsaye, ya akai ka fara sana’ar waka?

•Eh Toh Ni Daman Waka Ita Tanemeni Bani Na Nemetaba, Saboda Da Lokacinda Ina Primary Anamana Wasa Da Wake-wake musamman ranan P.E, Toh Daganan a hankali ahaka Na taso harna farajin wakokin mawaka irinsu billy’o da sauransu, Nima Kawai sai nake Kwaikwayonsu daganan harnaji Zan Iya Raira tawa Na kaina.

PRIME TIME NEWS: Mutane da dama sunsanka akan harkar waka, amma kuma akan hangi fuskar ka cikin wasu Bidiyo musamman na wasan barkwanci ( Comedy videos). Wannan karin haske za kaiwa masu karatu?.

 

•Eh Kafin Na Fara waka Nayi comedy da dama Saboda shi ma Comedy Abu ne Da nake Ra ayin yi badon komaiba sai dan in Nishadantar da al’umma dakuma ilimantarwa.

 

PRIME TIME NEWS:Yazuwa yanzu, kayi wakoki a kalla guda nawa kuma ka kai shekara nawa da fara shiga studio ka rera waka?

• Izuwa Yanzu Nayi Wakoki sunkai Goma Sha Takwas (18) , nakai shekara Biyu (2) Da Fara Shiga Studio.

 

PRIME TIME NEWS :Cikin wakoki 18 daka yi, wacce ce tafi jan hankalin jama’a wadda kuma itace da haska ka ga mutane?

•Sunanta AMASA .

PRIME TIME NEWS: Wanne sako wakar ke dauke dashi?.

•Eh Toh Wakarde Na Magana ne Akan Irin mutanen da idan Ka Fara abu suke ganin bazaka cimmaba.

PRIME TIME NEWS: Akwai wakar ka ta Mome daban ne wacce ta jawo cece kuce tsakanin mutane suna ganin kamar kana habaici ne ga wasu mutane ko wadanda bakwa samun jituwa haka, kodai kana musu habaici ne kan cewa kai na daban ne. Mene ne ita wannan waka take nufi?.

 

•No Wancen Wakar Yadda Mutane ke Dauka Ba Hakantakeba, Ai Kowama DABAN NEH Missali Wancan Aikinsa Daban Da Wannan, Wacce Kwalliyarta Daban Da Wacce Toh Kaga kowa daban da Kowa 😁 Nayi Wakarne Kawai Saboda nima DABAN NEH.

 

PRIME TIME NEWS: Wanne kalu bale ka samu a harkar waka zuwa yanzu?.

 

•Gaskiya Ban Taba Fuskantar Kalu Bale A Fannin Waka.

PRIME TIME NEWS: Wadanne nasarori kasamu a waka dama wasannin barkwancin da kakeyi?

•Nasara dai Ita ce ta Mosoya Da na Samu Dakuma Abokai Wanna Kadai ya isheni duk wata nasarori.

PRIME TIME NEWS: Mutane kanyi tambayoyi ga mutane irinka musamman masoya. Kai wacce tambaya mutane suka fiyima wanda har ka gaji da amsa su?.

•‘’_Kai Dan Wani Gari Ne_’’ Nasha Amsa Wannan Tambayan.

PRIME TIME NEWS: Akwai matsalolin rashin tsaro, garkuwa da mutane dama satar dalibai da ake fama dashi a Najeriya musamman a yankunan Arewa da kuma Arewa Maso Gabas. Wacce gudun mawa kake da ita ko shawara a matsayinka na dan kasa don ganin an magance wannan matsala?

•Toh Gaskiya Abune Da Kafin In Fada Wasu Sunrigani Fadi, soboda Haka Ni Tabakina Addu’ace Allah Ya Bamu Lafiya Da Zaman Lafiya A Kasarmu Nigeria Baki Daya.

PRIME TIME NEWS: Wacce shawara kake da ita ko kira ga yan uwa matasa?.

•Matasa Mu Dage Da Neman Ilimi Don Mune Zamu Gyara Gobenmu, Kuma Mu Kama Sana’a Mudaina Zaman Banza.

-Daga karshe,Wanne albishir zakaiwa masoyanka kan sabbin wakokin da zakai masu zuwa?.

•Albishirin shi ne Wani abinda basai Sunji ba Zamma Kowa Bazata.

PRIME TIME NEWS: Ga masu neman wakoninka ta ina zasu iya samunsu cikin sauki?.

•Za a Iya Samu a YouTube Channel Na
https://youtube.com/channel/UCLvQ0bcvlEoRT_1e43uTwmw

Kokuma Audiomack
https://audiomack.com/mome-neh-1.

PRIME TIME NEWS: Wanne koma baya ko cikas mawakan Hip hop kuke samu a bangaren aikinku?

•Eh Toh Wasu Daga Cikin Manyan Mawakan Hip-hop basa duba irinmu upcoming artist.

PRIME TIME NEWS: Wanne irin duba kenan?

•Irin Sudinga Janmu jikinsu tunda sumafa baiwarda Allah ya basu shi yabamu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here