Jakadan Kasar Canada ya bukaci Gwamnatin Najeriya ta Kawo Karshen Cin Zarafin Mata tare da Samar da aikin yi ga matasa

0
323

Mai rikon mukamin Jakadan Kasar Canada a Najeriya, Mista Nicolas Simard ya bukaci gwamnatin tarayya ta karfafa tsaro da kawo karshen nuna banbanci tsakanin jinsi gami da samar da aikin yi ga yan kasa.

Jakadan ya bayyana hakan ne yayin taron wayar da kai kan kawo karshen nuna wariyar jinsi a Kano wanda Kungiyar dake yaki da nuna wariya da cin zarafi ta Connected Development on a Project Galvanising Masa Actions Against Gender Based Violence ta shirya a Kano.

 

 

Jakadan Kasar Canada a lokacin da ya ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero

Mista Nicolas ya kara da cewa mata da dama a Najeriya sun fuskanci nuna wariya ko cin zarafi sau daya ko fiye da haka.

“A tallafin da ofishin jakadancin Canada dake Najeriya yake badawa, zamu tallafa tare da bada jari ga mata masu rauni da kananan yara da masu bukata ta musamma  da masu fama da cutar HIV da kuma hada gwiwa da gwamnati wajen ganin walwalar jama’ar Kano.

Anasa jawabin, Wanda ya kafa kungiyar ta Connected Development, Malam Hamzar Lawal ya kuduri aniyar bunkasa ayyukanta a jihar ta hanyar kira ga gwamnatin Kano ta sanya hannu kan dokar hana cin zarafin mutum tare da kare hakkin kananan yara da kuma dokar hana nuna banbancin jinsi.

Haka kuma, Babban Antoni Janar na jihar Kano, Barista M.A Lawan ya ce ma’aikatarsa na aiki tukuru da sauran hukumomi don ganin an aiwatar da dokar a jihar Kano, inda ya yi bayanin cewa, fannin da ma’aikatar tafi mayar da hankali sun hada da kawo karshen nuna wariyar jinsi da cin zarafin yara kanana  da kuma hana barace-barace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here