Hotuna: An Kama Wata Mata Gandiroba tana Lalata da Fursuna

0
278

An dakatar da Ma’aikaciya, Gandiroba dake aiki a gidan Gyaran Hali na KwaZulu-Natal a kasar Afrika ta Kudu bayan bayyanar bidiyonta tana lalata da wani Fursina a gidan Gyran halin.

“Mun aika da wasikar dakatarwa ga matar. An bata takardar a hannunta a yanzu an dakatar da ita kuma an fara bincike kan lamarin,” cewar mai magana da yawun hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasar, Singabakho Nxumalo.

A cewar Nxumalo, ikirarin da wasu ke yi na cewa mutanen biyun da aka kama ma’aurata ne ba gaskiya bane. “Ba Gaskiya bane, basu da alaka”.

Jami’ar da daurarran dai sun yi lalatar ne a gidan gyaran hali na KwaZulu-Natal.

“Yin Jima’i ko lalata tsakanin daurarru da Gandirobobi abin kunya ne da baza a hofantar da shi ba, ” cewar sashin kula da gidajen gyaran hali.


A Faifan Bidiyon da ya yadu a kafafen sadarwa na zamani, an hango mutanen na sumbatar juna daga bisa ni kuma suka fara lalata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here