DPR ya Gargadi Masu Gidan Mai a Kano Kan Siyar da Litar Man Fiye da Naira 162

0
111

Sashin Kula da Albarkatun mai na Kasa Reshen jihar Kano da Jigawa, (DPR) sun magantu cewar bazasu lamunci yadda wasu daga cikin masu gidajen mai ke kauracewa ka’idojin da Gwamnatin Tarayya Tarayya ta Sanya ba na tsai da daidaiton Farashin mai a Fadin kasa.

Cewar hakan ya fito ne ta Bakin controller a Hukumar reshen jihar Kano da Jigawa, Muhamamd Makera wanda ya ce a yau Laraba da suke Gudanar da Zagaye Domin tabbatar da cewar Masu gidajen man sun bi ka’idojin Dokar, sai dai kuma abun Takaici da suka ci Karo da shi shi ne wasu gidajen man basu bi ka’idojin ba, Domin kuwa an samesune da Karya Dokar sayar da man a kan Lita daya Naira 163 wasu kuwa 165 bayan da Gwamnatin Tarayyar kasar nan ta Kayyade Naira 162 kan ko wacce Lita.

 

Muhammad Makera yakuma Kara da cewar Yazama Wajibi wadanann Mutane suyi Biyayya ko kuma a hukuntasu daidai da Laifin da aka samesu dashi.

A Karshe  kuma ya jaddada cewar ko wane gidan mai yayi Amfani da Kayyayakin da ya kamata musamman ma a bangaren kashe gobara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here