Akanta Janar, Ahmad Idris Zai Gina Cibiyar ICT tare da Daukar Nauyin Karatun Daliban Gezawa

0
109

Daga Muhammad Bashir

 

Akanta Janar na kasa, Ahmad Idris ya ce aikin gina cibiyar bayar da horo kan fasahar sadarwa na zamani zai fara aiki nan bada jimawa ba a karamar hukumar Gezawa.

Ahmad Idris ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar lambar karramawa da gamayyar kungiyar al’ummar Gezawa ta bashi a garin Gezawa ranar Asabar.

Ya ce, cibiyar na daga cikin gudunmawarsa ga al’ummar Gezawa, inda ya kara da cewa hakan zai samar da aikin yi ga matasa domin dogaro da kansu da kuma ci gaban yankin.

“Na yi magana da Injiniyan da zai yi aikin a wannan safiya, ina mai tabbatar muku cewa fara ginin wannan cibiya zai fara cikin kwanaki 2”, inji shi.

“Ina so ku zabi mutane 5 a cikinku da za su hadu dani karfe 8, saboda ina son gabatar daku ga Injiniyan. Sannan ina son ku kawo min sunayen dalibai guda goma da suka kammala Sakandire suke da credits 5 zan dauki nauyin karatunsu a Jami’ar NOUN”,

Anasa jawabin, Sakataren gamayyar kungiyar, Dakta Gambo Haruna Yunusa ya yi bayanin wasu daga cikin matsalolin dake addabar al’ummar Gezawa da suka hada da Ilimi, Kiwon Lafiya, rashin aikin yi da tsaro.

Dakta Gambo ya yi kira yan asalin karamar hukumar ta Gezawa da su hada kai wajen maganin matsalolin ta hanyar tuntubar gwamnati da masu ruwa da tsaki.

Dakta Abubakar Shehu Gezawa wanda ya yi jawabi a madadin gamayyar kungiyoyin ya ce an shirya taron ne don girmama wasu muhimman mutane wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’ummar yankin.

” Wannan taro shi ne irinsa na Farko a karamar hukumar Gezawa kuma muna fatan zai cimma burin da yasa gaba”, inji Dakta Abubakar.

Sauran wadanda aka karrama sun hada da; Dakta Mannir Suleiman Gezawa, Darakta kula da lafiya na Jami’ar Bayero;Alhaji Muhammad Ya’u, Daraktan cibiyar na’ura mai Kwakwalwa ta Kano, Alhaji Garba Bako da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here