Yanzu-Yanzu: An Kara Sace Dalibai da Malamansu a Jihar Kaduna

0
307

Yan bindiga sun sace dalibai da malaman makarantar Firamare ta UBE a garin Rama na karamar hukumar Birin Gwari a jihar Kaduna.

Wasu mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya faru ne yayin da daliban ke tururuwar shiga makarantar da karfe 9 na safiyar yau Litinin.

Abddulsalam Adam, wani mazaunin yankin, ya ce yan bindigar sun zo ne a babura 12.

“An fada min cewa, an sace malamai 3 da wasu dalibai amma muna kokarin tabbatar da yadda ainihin lamarin yake. A yanzu yan Vigilanti da sauran samari sun tafi domin maganin yan bindigar”, inji shi.

 

Mohammady Birnin Gwari, shi ma ya ce yan’uwansa guda biyu nadaga cikin malaman da aka sace.

Ya bayyana sunan Umar Hassan da Rabiu Salisu Takau a wadanda aka kama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here