Batanci: Kungiyar JTI Ta Sha Alwashin Daukar Mataki Akan Abdul-Jabbar

0
123

Daga Muhammad Bashir

 

Kugiyar Jama’atul-Tajdidil Islam JTI ta gurfanar da Kwamishinan shari’a na Jihar Kano, Lawan Abdullahi, da kwamishinan ‘yansanda Sama’ila Shu’aibu Dikko bisa zargin gaza gurfanar da Abdul-Jabbar Kabara a gaban alkali.

Kungiyar ta bayyana wannan mataki ne a ranar Litinin yayin taron da ta shirya da manema labarai a birnin Kano.

A cewar daya daga cikin lauyoyin kungiyar, Barrister Abubakar Tanko sun dauki matakin ne, sakamakon gaza gurfanar da Abdul-Jabbar Kabara a Kotu, bisa furta kalaman batancin da ya ke yi ga Annabi Muhammad SAW.

Ya ce tunda ana zargin Abdul-Jabbar da aikata miyagun laifuka wadanda bata yarda dasu ba; domin haka za suyi amfani da doka wajen shigar da kara Kotu domin Kwamishinan yan sanda, ko kuma babban lauyan gwamnati su dauki matakin da ya dace, ko kuma a bamu dama, mu dauki matakin da ya kamata.

Ya ce karar da suka shigar shi ne kotu ta tilastawa wadannan mutane biyu da su gurfanar da Abuljabbar Kabara gaban kotu, ko kuma su basu dama idan ba za su iya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here