Sarki Sanusi Ya Zama Khalifan Tijjaniyyah

0
105

Darikar Tijjaniyya, mabiya tafarkin Sufaye ta nada tsohon Sarkin Kano, Muhamamdu Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyyah na Najeriya.

Mai magana da yawun tsohon Sarkin, Sa’adatu Ahmed, ta tabbatar da nadin nasa a wani rubutu da ta wallafa a shafin Facebook.

Ta ce an yanke shawarar nada Muhammad Sanusi II a matsayin Khalifa a daren Juma’a a garin Sokoto yayin taron Maulidin Sheikh Ibrahim Niass.

Matsayin Khalifancin dai a baya yana hannun kakan Muhammadu Sanusi sannan fitaccen malamin nan dan kasuwa, Khalifa Isyaku Rabiu shi ma ya rike matsayin kafin rasuwarsa.

A bayanan da shafin Wikepedia ya bayyana, Dariqar Tijjaniyya ta mabiya sufae ta faro asali ne daga Maghreb sai dai a yanzu tafi yaduwa a yankin Afrika ta yamma, musamman kasashen Senegal, Gambia, Mauritania, Mali, Guinea, Niger, Chad, Ghana, da Arewacin Najeriya.

Sannan akwai mabiya darikar a Kerala dake Kasae India.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here