Rikicin Shasha: Kwankwaso Ya yi Kira da Al’ummar Hausawa da Yarabawa su Zauna Lafiya

0
290
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yake gabatar da jawabi yayin bikin bude gadar sama a jihar Rivers

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga al’ummar Hausawa da Yarabawa dake Shasha a garin Ibadan na jihar Oyo kan su dawo da alakar dake tsakaninsu ta yan’uwantaka tun a da.

Ya yi kiran ne yayin da ya ziyarci al’ummar a garin Ibadan da yammacin jiya Juma’a.

Yayin da su ke jawabi a lokacin ziyarar da Kwankwaso ya kai, Baale na Shasha, Amusa Ajani, dan majalisa dake wakilyar mazabar Akinyele a majalisar dokokin jihar Oyo sun bayyana cewa rikicin ya faru ne sakamakon kin amincewa Bayerabe ya shugabanci kasuwar.

Ya ce Hausawa ne ke samar da shugaban kasuwar tun shekarar 1979, inda ya kara da cewa, yan kasuwa Yarabawa sun jaddada cewa dole ne sai Bayerabe ya zama shugaban kasauwar a wannan lokacin.

Olatunde ya ce rikicin ya faru ne saboda shugabancin kasuwar.

Olatunde ya fadawa Kwankwaso cewa: “Muna maraba da kokarinka na samar da zaman lafiya a Shasha. Tun shekarar 1979 yayin da aka kafa kasuwar Shasha, bamu taba samu wani rikici ba.”

Shima anasa jawabjn, Baale na Shasha, Amusa Ajani, cewa ya yi Hausawa da Yarabawa sun shafe shekaru suna rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Yayin da yake mayar da martani, Sanata Kwankwaso ya yi kira ga dukkan bangarorin da su zauna lafiya.

“Abinda na gani na kone shaguna, ba abu ne mai kyau ba ga kowa. A bar kowa ya yi kasuwancinsa da ya halatta. Ina kira ga dukkan wadanda abun ya shafa da su sake gina kasuwar Shasha”, inji shi.

A gidan Sarkin Shasha, Kwankwaso ya kara yin kira ga al’ummar Arewa da su ci gaba da zama lafiya da sauran al’umomi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here