Gwaggo ta Jinjinawa Fa’izu Alfindiki Bisa bada Tallafin Jari ga Matasa 701

0
130

 

Farfesa Hafasat Dr. Abdullahi Umar Ganduje Gwaggo, ta kaddamar da baiwa Mata Da Maza jarin Naira dubu goma ga kowanne mutun guda.

Mazaje 236 a yayin da Mata 467, Jimilla mutane 701 ne suka rabauta da tallafin na Mai girma Shugaban Karamar Hukumar Birni da Kewaye Hon. Faizu Alfindiki ya bayar, a kokarin shugaban karamar hukumar na baiwa mata da maza jari domin habbaka sanao’in su na dogaro da kai.

Bikin tallafin ya gudana ne a filin wasa na Sani Abacha, taron ya samu halartar Kwamishinan Kananan Hukumomi Hon. Murtala Sulen Garo, shugaban karamar hukumar Kumbotso Hasan Garban Kauye Farawa, Kwamishinan Matasa da wasanni Hon Kabiru Ado Lakwaya, MD Karota Hon. Baffa Babba Danagundi, Shugaban Jam’iyyar APC na Kano Municipal Hon. Sani Fata Sharada, Wakilan mai martaba sarki, Shugabar Mata ta Jamiyyar APC jahar Kano Hajiya Habiba Garba Ndalla, Speaker Hon. Baba Wapa, Masu baiwa gwamna shawara da masu ruwa da tsaki.

Matar gwammnan ta yabawa zababben shugaban bisa kokarin da yake tun kan yakai ga cika wata guda a ofis, ta ce  “hakika wanann abun yabawa ne kuma abun koyi, Nayi farin cikin jin yadda mutane suke cewa tunda ake Chairman a Municipal Ba’a tabayin Empowerment irin wannan ba wanda ya hada matasa masu kananun sana’o’i domin basu jari ba, kamar wannan sabon shugaban. tace ko a iya haka an samu canjin da muke bukata.

“Hakika wannan canjin ya biyo bayan kokarin mai girma Gwamna, na ganin cewa an tabbatar da nagartattun shuwagabanni kuma matasa wayanda zasu iya zaman ofis don sauraran koken talakawansu, Hon. Faizu Alfindiki ka kyauta kuma ka tabbatar mana da cewa zaka iya kuma ba zaka bamu kunya ba.”

Gwaggo ta bayyana cewa nan da wata 3 masu zuwa zata dawo domin tabbatar da cewa wayanda aka baiwa jarin sunyi abun da ya dace, tace za’a kara musu kuma za’a sake diban mutane 1,402 kari akan wayanda sukaci gajiyar a farko.

Mai girma kwamishinan Kanan Hukumomi ya yabawa Hajiya Hafsat bisa irin tallafin da take bayarwa, ya ce ba iya tallafi na kudi kawai take bayarwa ba, Ita Gwana ce wajen samar wa maza da mata aiki, a zahiri ita abar koyi ce ga masu san taimakawa al’ummar Jahar Kano, Sabo da duk wasu dabiun ta kyawawane. Muna Godiya.

Ya yabawa Hon. Faizu Alfindiki bisa wannan aikin da yayi kuma shima ya shiga cikin jerin Ciyamomin da suka kaddamar da wannan tallafi, yayi kira ga sauran ciyamomi suma suna jiran nasu tallafin domin ya zama wajibi a futo a taimaki alumma.

Ana sa jawabin shima, Hon. Faizu Alfindiki ya ce wannan bawai shi ne na karshe ba zasu kara zuwa nan gaba kadan domin kara zakulo wasu suma a tallafa musu, ya kara da cewa su masu biyayya ne ga abun da gwamnati take so, dukkan wanda yake tare da ahalin gwamna Ganduje to ya zama wajibi ya dunga gudanar da irin wannan.

Ya godewa Gwamna da Uwar marayu bisa irin damar da suka bashi kuma ya yabawa gwamishinan Kananan hukumomi Hon. Murtala Sulen Garo, domin dukkanin aiyukan da zamu gudanar na cigaba da sahalewar sa muke yi.

Ya yi kira ga wayanda suka rabauta da tallafin da su bi da shi da hanyar da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here