A yau Za’a yiwa Ganduje Allurar Rigakafin Korona

0
119

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a yau Alhamis zai kaddamar da fara rigakafin Korona a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano.

Za’a yiwa gwamnan allurar rigakafin tare da ma’aikatan lafiya dake sahun gaba.

Kwanaki biyu kenan da kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Ibrahim Aminu Tsanyawa ya karbi kaso na farko na rigakafin a madadin gwamnan.

Ya karbi rigakafin guda 209, 520.

A wani ci gaban kuma, gwamna Ganduje ya bayyana cewa suna sa ran yiwa kaso 70 na al’ummar jihar Rigakafin.

Ya bayyana hakan ne yayin taron wayar da kai da ya gudana jiya a gidan gwamnatin jihar tare da shugabannin dalibai a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here