Yanzu-Yanzu: Kano ta Karɓi Allurar Rigakafin Korona 209,520

0
358

Gwamnatin jihar Kano a daren jiya Talata ta karbi allurar rigakafin Korona 209, 520.

Yayin da yake karbar allurar rigakafin, a filin sauka da tashin jirage na malam Aminu Kano, Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce rigakafin kashi na farko zai fi mayar da hankali ne kan ma’aikatan lafiya.

Kwamishinan wanda ya wakilci gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnan ya karbi rigakafin kuma nan bada jimawa ba za’a yi masa allurar rigakafin.

A cewarsa, za su fi mayar da hankali wajen yiwa mutanen dake da matsalar rashin lafiya rigakafin yayin da kaso na hudu kuma za’ ayiwa kowa da kowa.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa kwamitin yaki da Korona zai tattauna yadda tsarin yin rigakafin zai kasance da kuma lokacin da za’a fara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here