Sanata Kwankwaso ya yi Bayani Kan Batun Takararsa ta Shugaban Kasa a 2023

0
307
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yake gabatar da jawabi yayin bikin bude gadar sama a jihar Rivers

Tsohon gwamman jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce a lokacin da ya dace zai bayyana muradinsa na yin takakarar shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Kwankwaso ya ce yanzu babban abinda yasa gaba shi ne taimakwa wajen ci gaban jam’iyyar PDP ta tsarin tafiyar darikar Kwankwasiyya ta hanyar samar da ilimi da aikin yi har zuwa shekarar 2023.

Ya yi bayanin hakan ne yayin da yake jawabi ga wasu kungiyoyin magoya bayansa Da suka kai masa ziyarar nuna goyan baya ga jam’iyyar PDP da Akidar Kwankwasiyya ranar Litinin a Abuja.

Ya fadawa magoya bayansa da su girmama sauran masu sha’awar yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP.

Idan za’a iya tunawa dai, Sanata Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, inda Atiku Abubakar ya kada shi.

Kwankwaso ya kuma bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Saraki, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a matsayin yan’uwa kuma abokan gwagwarmyar ceto Najeriya da sanyata a hanyar ci gaba.

“Dole ne na shawarci dukkan magoya bayana na PDP da tafiyar Kwankwasiyya da sauran masu fatan Alkhairi kan kar su soki duk wani dan takara ko shugaban jam’iyya a madadina, inda ya kara da cewa muradin jam’iyya shi ne gaba da muradin kashin kai”, inji Kwankwaso.

Yayin da yake jawabi a yayin ziyarar shugaban tawagar magoya bayan na Kwankwaso, Mista Emmanuel Bitrus ya ce sun amince da akidun Kwankwaso musamman a fannin ilimi, samar da aikin ga matasa da ayyukan ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here