Rundunar Vigilantee ta Buɗe Sabon Ofis a Sauna Kawaji Domin Yaƙi da Ɓata gari

0
187

Rundunar Vigilantee ta Jihar Kano ta ce ta Samu Nasarar Bude Ofishin Vigilantee na Shiyya a yankin Unguwar Sauna Kawaji Domin Fatattakar Bata Garin Matasa da ake Zargin Yan Fashi da Makami ne a Unguwar.

Babban Kwamandan Rundunar Muhammad Kabir Alhaji ne ya Bayyana hakan yayin da yake Gabatar da Jawabin Sa ga Manema Labarai a Yau.

Yana Mai Cewar, a Kwanakin Baya ne Aka Kama Wasu yan Fashi da Makami a Unguwar da Suka Shiga Wani Kamfani Suka Kwashi Kudi Sama da Miliyan Dari.

Wasu Daga Cikin Mazauna Unguwar Sun Bayyana Jin Dadin Su Dangane da Bude Wannan Ofishin na Vigilantee a Yankin Nasu, Suna Mai Cewar, yanzu Zasu Kwanta Barci Harda Munshari Sakamakon Sun Samu Ingantaccen tsaro a Yankin Nasu.

A Karshe dai Sun Bayyana Cewar, Zasu Baiwa Jami’an Rundunar Vigilantee Cikakken Hadin Kai Wajen Samar da Kayan Aiki harma da Basu Bayanan Sirri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here