Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kama Motoci na Miliyan 83 da basu da takardun Sheda a unguwar Hotoro

0
116

Hukumar hana Fasa Kwauri ta kasa shiyyar jihohin Kano da jigawa ta ce ta kama kayayyaki da kudin su ya Haura Naira biliyan biyar a watan Janairu da fabrairun shekarar 2021.

Kudin da Hukumar ta Bayyana yakai kimanin Biliyan biyar da Naira Miliyan Dari biyar da Ashirin da shida da Dubu dari Uku da Hamsin da biyar da Dari tara da Goma sha Hudu.

Babban kwanturolan Hukumar Reshen Kano da Jigawa shi ne ya Bayyana hakan A yau yayin Taron manema labarai da su ka Gudanar yau a shelikwatar Hukumar dake Unguwar bompai a Kano.

Hukumar ta kuma kama wasu manyan Motoci da suka Haura Naira Miliyan 83 a Unguwar Hotoro wadanda basu da takardun shaida kuma mallakin wasu manyan Mutane ne.

Wakiliyar Jaridar PRIME TIME NEWS, Nusaiba Abdulaziz Muhammad,  ta rawaito mana cewa Babban kwanturolon Hukumar ya ce zasu ci gaba da tabbatar da bin doka tare da Hukunta duk wanda suka samu da Laifin safara ba bisa kaida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here