Dalilan da Yasa Nura M. Inuwa Ya Gaza Cika Alkawarin da ya Dauka na Sakin Sabbin Wakokinsa

0
228

 

Daga Junaid Idris Gezawa

Jaridar Film magazine  ta wallafa labarin cewa fitaccen mawaƙi , Nura M. Inuwa ya bayyana dalilin sa na rashin fitar da fayafaye biyu na waƙoƙin sa a ƙarshen Fabrairu kamar yadda ya alƙawarta.

A watan jiya dai fastocin kundin waƙoƙin sa sun karaɗe soshiyal midiya wanda ya sa aka yi tsammanin mawaƙin zai saki kundaye biyu na waƙoƙin a ƙarshen watan kamar yadda ya yi wa masoyan sa albishir a cikin wata hira da ya yi da yan jaridu.

Sai ga shi har an haura mako ɗaya a cikin sabon wata amma an ji shiru.

Masoyan Nura sun zaƙu su ji sababbin waƙoƙin sa ne domin an ɗauki tsawon shekaru biyu su na jira.

Ana haka ne kwatsam, sai mawaƙin ya fito da wata sanarwar ban-haƙuri game da gazawar sa kan wannan al’amari a shafin sa na Facebook, amma bai bayyana dalili ba.

Kan haka ne muka tuntuɓe shi domin jin dalilan da ya sa bai saki waɗannan album ɗin nasa guda biyu ba kamar yadda ya alƙawarta.

A tattaunawar sa da wakilin mu, Nura M. Inuwa ya ce, “Dalilin da ya sa ban saki albam ɗi na ba masu suna ‘Ni Da Ku’ da kuma ‘Lokaci’ shi ne mu na so ya kasance lokaci guda mun sake su a gari a kan sidi da kuma sauran guraren da mu ke so na yanar gizo, yanda zai zama kowa ya samu ba tare da an samu jinkiri ba ta yadda wasu za ka ga sun riga wasu samu; misali, za ka ga akwai da dama daga cikin masoya na wanda ba sa iya ɗaukar abu daga kan yanar gizo.

“Wannan dalilin ne ya sa mu ke so mu je har gurin masu ‘downloading’ da kuma ‘yan kasuwa mu tattauna domin mu sake su a kowace kafa a kuma lokaci guda.

“Sannan akwai matsalar da mu ka samu daga kamfani na rashin kammala abubuwa da dama na wannan kundin nawa.”

Shin da ma can ba su gama shiryawa ba amma ya bayyana ƙarshen Fabrairu a matsayin lokacin da za su saki kundayen? Sai ya amsa da cewa: “Mun shirya da kuma sanin cewa lokaci zai ishe mu mu yi har mu cimma saki a ƙarshen watan na Fabrairu. Da mu ka tattara mu ka kuma tura kamfani, sai ya zamana mun samu wata tangarɗa. Shi ya sa dole aka samu ɗan bambanci.

“Kuma a yau ne mu ke sa ran jin ta bakin shi kamfani kan wannan al’amari da kuma lokacin da za su ƙarasa kawo mana kayayyakin mu.

“Sannan masoya na ba na jin hakan zai sa su ƙosa domin yardar da su ke da ita a kai na ba na jin za ta ba su wani sarewa a kan haka.

“Amma dai na san da cewa masoya na sun ƙagu su ji waƙoƙi na. Da haka ne kuma na ke ƙara ba su haƙuri kan wannan tsaiko da aka samu.”

Bugu da ƙari, Nura ya bayyana cewa, “Komai idan ɗan’adam ya nufa zai yi idan Allah bai amince ba dole ya haƙura, kamar yadda mu mu ka tsara cewa lokaci kaza za mu yi abu cikin yaddar Allah, kuma bai nufa ba. Ina fatan jinkirin ya zama alkairi.

“Sannan kuma masoya na su ci gaba da jira, don ko a yau kamfani ya ba mu tabbacin cewa ya kammala komai.

“Ina kuma bada tabbacin da yardar Allah a cikin watan Maris ɗin nan da mu ke ciki komai zai kammala kuma kowa zai samu waƙoƙi na na wannan shekarar in dai ya buƙaci haka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here