Tsohuwar Matar Attajirin Duniya Jeff Bezos ta Auri Malamin Makaranta

0
111

Attajiran nan Mackenzie Scott, tsohuwar matar shugaban kamfanin Amazon, Jeff Bezos ta auri malamin kimiyya a makarantar ‘ya’yanta shekaru bayan rabuwarsu da Jeff Bezos.

An samu labarin aurenta da Dan Jewett ne ta hanyar Shafi Giving Pledge.

“Dan babban gaye ne, kuma ina farin ciki da jin dadi ga dukkansu”, inji Mista Bezos.

Misis Scott wacce ke da adadin dukiyar da ta kai Dala Biliyan 53 kamar yadda mujallar Fobes ta wallafa, ta bayyana kudurinta na bayar da kyautar mafi yawa daga abinda ta mallaka.

Misis Scott ta zauna Aure da Mista Bezos tsawon shekaru 25 kuma tallafa masa wajen kafa kamfanin Amazon 1994. Kuma ta wallafa litattafai biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here