Ranar Mata ta Duniya: Maza na Sukar Batun Samar da Daidaito Tsakanin Jinsi tare da bawa Mata Jagoranci

0
184

Daga Junaid Idris Gezawa, Salisu Hamisu Ali

 

Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara a matsayin ranar Mata ta Duniya.

Sashin Hausa na BBC ya wallafa yadda ranar matan ta duniya ta samo Asali da shekarar da aka fara bikin ranar mata.

Ranar Mata ta Duniya, ta samo asali ne daga kungiyar kwadago don neman ta kasance cikin ranakun da majalisar Dinkin Duniya ta san da su a ko wace shekara.

An kuma kafa ta a shekarar 1908, lokacin da mata 15,000 suka gaudanar da gangami a fadin birnin New York suna neman a rage musu yawaan lokutan aiki, da albashi mai kyau, da kuma ba su ‘yancin kada kuri’a.

Shekara guda bayan haka ne jam’iyar Socialist ta Amurka ce ta ayyana Ranar Mata ta Duniya ta farko.

Shawarar mayar da ranar ta kasance ta duniya baki daya ta samo ne daga wata mata mai suna Clara Zetkin.

Ta bullo da shawarar ne a shekarar 1910 a wani babban taron kasa da kasa kan mata a birnin Copenhagen.

Mata 100 ne suka halarci taron daa kasashe 17, kuma suka amince da shawararta nan take.

An fara gudanar da bikin ne a shekarar 1911, a kasashen Austria, da Germany da kuma Switzerland.

An kuma gudanar da bikin cike shekaru 100 da bullo da bikin ranar a shekarar 2011, don haka a cikin wannan shekarar za mu yi bikin cika shekaru 110 na fara bukin Ranar Mata da Duniya.

A shekarar 1975 ne aka tabbatar da bikin ranar a hukumance, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta fara bikin wannan rana.

Taken bikin na fako da Majalisar Dinkin Duniyar ta tsayar a shekarar 1996 shi ne “Bikin tuna baya, tsara rayuwa ta gaba.”

Ranar Mata ta Duniya ta zama ranar bikin duba halin da mata ke cikin a tsakanin al’umma, a fannonin siyasa, da tattalin arziki, yayin da a tushen siyasar hakan na nufin yajin aiki, kuma a kan shirya gudanar da gangami don fadakarwa game da ci gaba da nuna wariya.

Sai dai Majalisar dinkin duniya da masu fafutuka a kasashen yamma sun sha yin kira da a samar da daidaito tsakanin jinsin maza da mata tare mika jagoranci ga mata.

A kan wannan batu ne jaridar PRIME TIME NEWS ta tattauna da Wasu Maza da mata kan yaya suke kallon wannan kiran da majalisar dinkin duniya ke yi na samar da daidaito tsakanin jinsi.

Ga Kadan daga Ra’ayoyin Wadanda Wakilinmu, Junaid Idris Gezawa ya tattauna da su:

 

Sadiq shehu Doguwa (sadiq mai gashi)

“Kai tsaye bana goyon baya saboda hakan ya sabawa addinin musulumci, Allah subhanahu’wata’ala yana fada acikin littafin sa cewa “Maza suna gaba da Mata”.

“Dan haka babu wani dalili da zai saka wani ko wata ya sabawa wannan maganar matukar yana mai imani da ranar karshe.

“Ina mamakin mutanen da zakaga su na ta dagewa akan dai-dai to ga maza da mata, wanda hakan ba zai taba yiwuwa ba.

“Saboda su kan su turawan da suka zo da maganar ba sa aikatawa a aikace kawai suna kawo mana rudune saboda sun san addinin mu yayi hani akan haka

“Yanzu ka dauke kasashen turawan zakaga babu hakan a aikace sai dai fada a baki da takarda,

Yanzu bari na bada wani misali:

“Mutane ne guda biyu suke da kamfani daya sai ya dauki maza guda 50 aiki shi kuma dayan ya dauki mata 50 aiki

“Shin wacce ma’aikata ce za’afi samun ci gaba?”

“Kafin ka bada amsa yaka mata kayi nazari kan wadan nan abubuwa da zan fada:

1- Idan mace ta dauki ciki dole aikin da takeyi zai ragu

2- idan cikinta ya girma dole za’a bata hutu.

3- idan ta haihu za’a bata hutun raino.

“Duk acikin wadan nan hututtukan kar ku manta ana biyansu albashi amma basa zuwa aiki.”

 

Abubakar Sadiq Sulaiman

“Ina goyon bayan samar da daidaito tsakanin mata da maxa amma tawani bangaren kamar inda yake lamarin duniya ne saboda yadda zamani yake canzawa sai dai ansan cewa ba komi mace zata iya yi ba musamman ma a yankuna irin namu masu al’ada daban da na sauran kasashe Dan haka ina goyon bayan abasu iyaka abinda za su iya amma banda jagorancin alumma sai da abasu damar yin wakilci”.

 

Surayya Ibrahim

“Ni a ganina tabbas ana tauyewa mata hakkinsu wajen jogaranci, mu ne muke bayar da tarbiya a gida kaga kuwa babu abinda zai sa baza mu iya Jagorantar al’umma ba”.

 

Hafsat Musa

“Ina goyan a samar da daidaito domin hakan zai rage irin cin zarafin da wasu mazan ke wa mata”.

 

Habib Hassan Gado.

“Ni a ra’ayina mace bai kamata a daidaitata da namiji ba, mace halitta ce mai rauni matuka, tun daga sanda aka haifi mace har ta mutu a karkashin namiji take, idan tana yarinya tana karkashin iyayenta, sanda ta girma kuma tana komawa karkashin mijinta, idan ta tsufa kuma tana komawa karkashin kulawar yayanta,ita mace kullum a karkashin kulawar namiji take,saboda rauninta a komai na rayuwa.

“Duk duniya babu wani gida mai rauni lalatacce wanda ake cin amanar juna kamar gidan gizo-gizo, ya zamo lalataccen gida ne saboda mace ce take gina gidan ba namiji ba,kuma ita ce shugaba a gidan, kowa na gidan a kasanta yake.

“Kuma ko a mutane abu ne na kaskanci a cewa mutum Dan mace ne,ko kuma yar mace ce,ana nufin mace ce take jan ragamar gidansu hakan kaskanci ne.

“Saboda haka ni a ra’ayina mace ta zamo shugaba a bata jagoranci ba za a samu sakamako mai kyau ba, kamar a ce namiji ne jagora.”

 

A yayin da ake bikin ranar Matan ta Duniya ita ma fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ta fitar da jerin sunayen Mata 50 dake kushe cikin gwamnati shugaban kasa Muhammadu Buhari, kama daga Ministoci, mataimaka na musamman da shugabannin hukumomi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here