Ina Amsa Kiran Waya daga Ƴan Mata Fiye da Sau Dubu 1 a Kowacce Rana – Salbas

0
796

Daga Junaid Idris Gezawa

Fitaccen Mai Karatun Litattafan Hausa a gidajen Rediyo, Abdullahi Muhmmad Salbas ya bayyana cewa ya na amsa kiran waya na masoyansa fiye da sau Dubu a rana daya.

Matashin Dan Jaridar ya bayyana hakan ne a tattaunawar da yayi da wakilin Jaridar PRIME TIME NEWS, Junaid Idris Gezawa inda ya bayyana cewa har kyautar Mota ya samu daga Masoyansa.

Ga Yarda Tattaunawarsu ta kasance:

 

-Koda yake sanin kowa ne cewa kai shahararre ne kuma sananne a fannin aikin jarida musamman bangaren karanta littattafan Hausa. Amma mai karatu zai so yaji daga bakinka a takaice shin wane ne Salbas?.

 

•Toh Assalama Alaykum ,sunana Abdullahi Mohd Salbas ,an haife ni a Kano anan Kuma na girma nayi karatuna tin daga nursery, Primary, Secondary Kai harma da jami’a duk da dai kafin nayi degree na sai Da na yi diploma, har ta kai ga na samu aikin jarida.

– Malam Abdullahi ya akai ka tsinci kanka a aikin jarida?.

• Toh ,Alhamdulullahi kasancewar kowanne Dan Adam da yadda Allah ke kaddara yadda rayuwarshi za ta kasance ,hakan ce ta kasance domin kuwa na shigo aikin jarida ta dalilin Industrial Training (I.T) Da na fara yi a gidan radio tarayya , pyramid radio 103.5 FM idan aka tarbe ni a sashin labarai da al’amuran yau da kullum Kuma sashin da ake gabatar da wani shirin mai taken ZARE DA ABAWA hakan yasa na kasance daya daga cikin masu kawo rahotanni na mussaman a wannan sashi da taimakon Mai shirya Shirin Kuma ogana Adamu dabo Adamu Wanda shi ne mutum na farko daya fara Dora Ni a hanya sai Kuma program manager a wancan lokacin mallam Dan Bala Gwarzo, duk da kasancewar a wannan lokaci ba Wai aikin jaridar nake karantawa ba makarantar da nake .Amma Dan aikin jaridar ne ya ingiza Ni zuwa gidan radio har na Kai matakin da nake a yanzu .Wanda Jajircewa da taimakon Allah yasa na ci nasara.

– Akwai wasu Masu sauraron shirye shiryenka dake ganin kafi kwarewa a fannin karatun littafi wanda shi ne mutane sukafi saninka dashi. a cikin akan ji kana salo daban- daban cikin salon da kake harda Sauya murya daga ta maza zuwa ta mata, daga ta mata zuwa tsoffi ko yara. Shin ka samu wani horo na musamman ne akai?.

 

• A’a gaskiya ban samu ba, kasancewar baiwa wani Abu ne da Allah ke azurta bawa da shi wasu haifar su ake da ita wasu Kuma sai sai sun zo duniyar suke samun damar sanin baiwar da Allah yayi musu A don haka misalin hakan ne ya faru da ni dan ni gaskiya ba Wai ganin dama bane yasa na zabi karatun littafi ba an dai bani a matsayin na gwada ko Zan iya sai Naga ya Dace na kawo wani salo da zai banbanta da karatun sauran makarantan sauran gidajen rediyo hakan yasa na kawo wani salo da ba kowa ke yin irin shi ba Kuma ya banbanta wato Dana sauran wannan salo shi ne na canza murya na kala kala.

– Kana da dumbun masoya dake bibiyar shirye shiryenka masu tarin yawa. Daga wanne bangare na jinsi kafi amsa kiran waya da fatan alkhairi?.

•To ai Zan iya cewa sai a Kira wayna a Rana yafi sau dubu duk da mafi yawancin su Mata ne ,idan za su bugo su ce suna min fatan alkhairi wasu Kuma flashing su ke ,duk da cewa mazan ma ba ‘abar su a baya ba wajen Kira da fatan alkhairi.
Baya ga kira ma sukan biyoni ta shafuka na na sada zumumta ta WhatsApp, Instagram, Twitter,da dai sauransu Dan Mika sakon gaisuwa da fatan alkhairi Hadi da samun nasara a rayuwa.

-Wacce kyauta ce wacce aka yi maka da ba zaka iya mantawa da ita ba?

• Hhhha! Kai dai Bari ai abin ba ‘a magana domin har da akwai wadanda sukai min kyautar mota ta Hawa kirar Ford focus wacce ita nake Hawa ma yanzu, ga Kuma masu turon kati dama kudi abin dai da bazan manta ba shi ne filin da wasu suka siya min a wata unguwa Wai ita Yan dodo dake kano.mutane na Kuma Yan KarKara sun Sha kawo min irin kayan mu na kauye kamar kuka ,gero da dai sauran su, ai Ni Babu abin da zancewa Allah da masoya na sai godiya.

– Mene ne sirrin daukakar Salbas?

 

• Allah ne yayi mini komai dadin dadawa Ai sirrin dauka ka na Bai a
wuce kyakyawar alakar dake tsakani na da iyayena ba ababan kaunata ba.

-Wanne kalu bale kasamu da kuma nasarori cikin ayyukan ka?.

 

•To ai dama duk wani Wanda ya taka matsayin da nake ciki ko Kuma ya tsunduma duniyar SHAHARA tofa Dole ya ci Karo da matsaloli ta bangarori daban- daban , duk da dai Ni nasarori na sun rinjayi kalubale na. Kasancewar na bada lamba na a gidan rediyo saboda masu neman Karin bayani ko tambaya ko turo sako wasu suka amfani da wannan damar da su bugo su Zage Ni tare da fadar munanan kalamai a Kai na ,wasu Kuma da wasu bakaken manufa na San ra’ayinsu da son zuciyoyinsu za su kira ni .Kai! da akwai lokacin da na daga waya abin da na fara ji zagi ta uwa ta uba. Wai Ni Dan daudu ne gashi Nan dai Wanda hakan na nufin nassara.

Nasarori ma Kuma ai su ne ma suka fi yawa Dan sai na kwana mu tashi ban Gama fadar su ba to Alhamdulullah. Allah yamin baiwar da arzikin mutane Dan jama’a rahamace kafin Naga Wanda ya kushe Ni daya sai Naga dubun masoya na Babu adadi, Saboda tsabar soyayya wasu murya na ma kadai suka ji suke Gane cewa eh tabbas wannan fa Salbas ne , sannan muma ta dalilin wannan sana’a nawa na karatun littafai a gidajen radio da talabijin manyan kamfani kan Kira Ni wajen yi musu tallace tallacen da sauran su wasu ma aiki suke min wasu Kuma Kira na suke suyi mini abin arziki .Kai wasu ma kawai zasu Kira Dan fatan alkhairi tare da Addu’ar wanyewa lafiya. Sai Kuma abubuwan more rayuwa da na samu Kama daga muhalli,da abin Hawa duk na same su ta dalilin nasarar da na samu ta arzikim mutane.madalla ga mutane na Yan Amana ta.da a duniyar Nan duk Wanda yace Yana sonka to ya Gama yi maka komai.

-Wanne nau’in abinci kafi so?

•Hhhh! wake da shinkafa da salad , tomato,cocumba ,da dai hadin salad ya sha awara ko kifi a sama.

– Wacce shawara za ka bayar don kawo karshen matsalar tsaro da kuma sace sacen dalibai da ake fama dashi a Najeriya Musamman a yankunan mu na Arewa?

•To shawarar da Zan bawaa gwamnati da dukkanin masu madafin iko shi ne ,su ji tsoron Allah su sani duk abin dake faruwa Allah Yana nan madakata Yana jiran su kuma zai tambaye su yadda suka tafiyantar da mulkin su ,sanan Kuma kamata ya yi gwamnati ta san inda matsalar ta ke ta yadda zata San yadda zata bullowa Al’ amarin dai Kuma mu rike addu’a wacce ita ce makamin mumini tare da gyara tsakanin mu da mahalicci mu Allah.

-Wanne sako kake dashi na karshe ga masoyanka da kuma sauran matasa yan uwanka?.

•To Ina musu fatan alkhairi,Ina kaunarsu kamar yadda suke kauna ta , Allah ya bar zumunci domin da bazar su nake rawa.idan babu su babu ni, idan babu ni Babu su nagode Inawa kowa fatan samun nasara a rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here