Gwamnatin Kano ta Keɓe Cibiyoyi 509 don yin Allurar Rigakafin Korona

0
255

Gwammatin jihar Kano ta samar da cibiyoyin yin allurar rigakafin Korona guda 509 a jihar.

Shugaban tawagar kwararru kan yaki da annobar Korona, Tijjani Hussaini, ne ya bayyana hakan a yau Litinin a taron wayar da kai da jami’an tsaro a gidan gwamnatin jihar Kano.

A jawabin da ya gabatar mai taken “Rigakafin Korona: tsarin raba shi a jihar Kano’ Tijjani Hussaini ya ce : A jihar Kano, mun samar da cibiyoyin lafiya 509 da za’a yi amfani da su a matsayin cibiyoyin allurar rigakafin Korona.

“Za mu yi amfani da asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Asibitin Muhamamdu Abdullahi Wase da Asibitin Kashi na Dala”.

Ya ce akwai matakai 4 na yin rigakafin a Kano.

” Mataki na farko zai fi mayar da hankali ga ma’aikatan lafiya dake aiki, mataki na biyu sauran ma’aikatan lafiya da mutanen da suka haura shekaru 50, mataki na 3 kuma zai mayar da hankali ga mutanen dake fama da rashin lafiya sai mataki na 4 zai mayar da hankali ga dukkan mutane”.

Ya bukaci mutane su yi rijistar neman allurar rigakafin ta yadda gwamnatin tarayya za ta turo allurar dayawa zuwa Kano.

Anasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwaamati ta yanke shawarar fara wayar da kan ne da jami’an tsaro, kasancewarsu su ne sawun farko a cikin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here