Majalisar Wakilai ta Bada Umarnin Bude Filin Jiragen Sama na Malam Aminu Kano

0
183

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta bude filayen sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Shugaban masu rinjaye na majalisar kuma mai wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa, ya ce sake bude filin jirgin ya zama dole idan ana san habbaka tattalin arzikin kasaran.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar yan majalisar zuwa filin jirgi.

Acewarsa, ziyarar tasu ta duba filin jirgin ya biyo bayan tattaunawar da su ka yi da ministan jiragen sama, Hadi Sirika a ranar Alhamis.

“Muna sane da cewa an rufe shi ne tare da sauran filayen jirage na duniya kan batun da ya shafi cutar Korona, wacce ta zama babban kalubale a fannin lafiya a wannan kasa.

” Idan ka duba al’amarin, Jihar Legas da birnin tarayya Abuja suna da masu kamuwa da cutar da yawa fiye da Kano. Ba muma da sabon nau’in cutar anan Kano, amma an har yanzu filin sauka da tashin jiragen yana kulle.

“Muna damuwa matuka kan tabarbarewar kasuwanci a Kano wanda rufe filin ya haifar. Yan kasuwa da dama sun yi asara.

“Mun tattauna da minista ya bamu dalilai na aiki sannan ya tabbatar mana cewa za’a bude filin jirgin nan bada jimawa ba”, inji shi.

Yayin da yake zagayawa da yan Majalisar, Manajan Darakta na hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya(FAAN), Captain Yadudu, ya tabbatar da cewa za’a bude filin jirgin nan ba da jimawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here