Alkalin Da Ya karanta hukuncin Shari’ar Abba Gida-Gida da Ganduje Ya Mutu

0
8260

Alkalin kotun Koli wanda ya karanta shari’ar zaben gwamnan jihar Kano tsakanin Abba Gida-Gida da Ganduje, Sylvester Ngwuta ya mutu.

Wasu majiyoyi daga kotun koli sun tabbatar da cewa, Ngwuta ya mutu da safiyar yau Lahadi a gidansa dake Abuja yana da shekaru 70.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ngwuta ya shirya yin ritaya a 30 ga watan Maris na shekarar 2021.

Kamfanin dillacin labarai na kasa ya rawaito cewa Mai shari’a Ngwuta an haife shi 1951 a Amofia-Ukawu, a karamar hukumar Onicha dake jihar Ebonyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here