Bai Dace a yiwa Ƴan Bindiga Afuwa ba – Gwamna Masari

0
395

Daga Junaid Idris Gezawa

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce yan bindigar dake kashe yan Najeriya a Arewa basu chanchanci ayi musu afuwa ba.

Masari, ya fadi hakan ne yayin da yake mayar da martani ga Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musulunci dake neman ayiwa yan bindiga afuwa.

Gumi, wanda ke samun damar zuwa inda yan bindiga suke ya na ci gaba da neman ayi musu afuwa.

A wata tattaunawa, Gwamna Masari ya ce yan bindiga sun ha’inci gwamnati bayan yunkurin yi musu afuwa a baya.

“Afuwa ga wa? Kaga, Gumi yana neman ayi musu afuwa a 2021, mun yi a 2016, a takaice akwai abinda yakamata a koya daga gare mi”, inji shi.

” Yayin da muka fara tattaunawa a 2016, kashi 95 na makiyaya dake rayuwa a daji ba masu laifi bane amma yanzu ya yanayin yake? Yawancin makiyayan dake daji yan bindiga ne.

“Gumi wa’azi zai yi musu kan su ji tsoron Allah; su san hadarin da yake tattare da kashe rai ba wai neman yi musu afuwa ba saboda ko dabbobi ba a yarda a kashe su cikin rashin adalci ba balle kuma dan adam. ya kamata ya sanar da yan bindigar kimar addininsu”.

Ya kara da cewa babu wani abu sabo dangane da abinda yan bindigar ke nema amma mafi muhimmanci , ” basu da wata akida ko manufa”.

“Shin dukkan mu muna cikin farin ciki a Najeriya? Shin ana nufin duk wanda baya cikin farin ciki zai dauki makamai ya dinga farwa mutane?, su yan bindigar suna cewa an watsar dasu a Najeriya”, inji gwamnan.

” Barawo barawo ne kuma mai laifi mai laifi ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here