Yanzu-Yanzu: “Na taba Kamuwa da Cutar Korona”, Inji Obasanjo

0
157

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a yau Juma’a ya bayyana cewa ya taba kamuwa da cutar Korona.

Ya bayyana labarin hakan ne a Abeokuta, jihar Ogun yayin da yake jawabi a taron taya shi murnar cika shekaru 84 da haihuwa.

Taron an yi shi ne Dakin karatu na Olesegun Obasanjo Presidential Library.

Obasanjo ya ce “Zai baku mamaki cewa na kamu da cutar Korona. Na kira su suzo su yimin gwaji ranar Asabar, ban samu sakamakon gwajin ba sai ranar Laraba kuma ya nuna cewa ina dauke da cutar Korona amma banga wasu alamu na cutar ba.

” yayin da suka dawo bayan kwana 3 sun yi min gwaji suka ce yanzu bana dauke da cutar, kwana 3 kenan bayan na kamu da cutar.”, inji Obasanjo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here