Rayuwar Ma’aurata: Abubuwan Da Yakamata Miji ya yiwa Matarsa Mai Dauke da Juna Biyu

0
164

Babban burin ma’aurata shi ne samun ‘ya’ya wadanda za su tashi su kwanta su yi wasa a gidansu.

‘Ya’ya wata kyauta ce daga Allah babu kokwanto akan hakan, kuma dukkan Ango da Amarya suna da burin zama iyaye.

Mata su ne jaruman da Allah ya kaddara za su dauki ‘ya’yaye a cikinsu tsawon wata 9.

A matsayinka na cikakken mutum mai nuna soyayya, wanda ke kula da matarsa, yakamata ka sani duk matar dake dauke da juna biyu abar tausayi ce. A taikace suna matukar shan wahala a tsawon watanni 9 dauke da juna biyu. Wasu na ganin cewa abinda mata ke jura tsawon watanni tara tare da yin nakuda wajen haihuwa maza baza su iya jurararsa ba.

Shi yasa duk mace mai juna biyu ta chanchanci kulawa daga mijinta da duk wadanda suke tare da ita saboda tana shan wahala a halin rayuwatar. A wannan rubutu akwai abubuwa 8 da miji zai yiwa matarsa mai dauke da juna biyu domin kula da ita.

1. Kayi kananan abubuwa na tafiyar da gida kamar wanke-wanke, shara da wankin kaya.

Idan matarka na dauke da juna biyu kar ka barta tayi ayyukan wahala a gida. Idan da yuwuwa ka dakko mata yar aiki da zata tayata aikin gida, idan baza ka iya hakan ba kayi mata da kanka.

2. Ka dinga yiwa kafafunta tausa da sauran bangarorin jikinta a kullum.

Mace mai dauke da juna biyu tana gajiya a kodayaushe koda bata yi aikin komai ba. Tana gajiya a kullum kuma tana bukatar hutu, shi yasa take bukatar ayi mata tausa.

3. A duk sanda ka fita aiki ka tabbata ka kira wayarta duk awa daya ko biyu.

A kodaya yaushe ka dinga tuntubar matarka kada ka manta da ita.

4. Kayi hakuri da ita a kullum.

Mata masu juna biyu a kodayaushe suna daukar zafi don haka dole ka dinga hakuri da ita . Kar ka sata kuka.

5. Ka dinga bata labaran nishadi da ban dariya.

A kodayaushe kayi kokarin sanya matarka cikin farin ciki tare da sata a kyakkawan yanayi. Kasancewa cikin mummunan yanayi zai shafi lafiyarta.

6. Ka girka mata abincin da take so yayin da take jin yunwa.

Kayi kokarin zuwa dakin girki tare da girka mata abinci mai dadi.

7. Ka yi mata kyautar ban mamaki.

Matarka zata kasance cikin farin ciki a duk sanda ka bata kyautar bazata, kayi kokarin yi mata hakan sau daya a duk mako.

8. Kayi magana da jaririn dake cikinta.

Bincike ya nuna cewa yayin da ma’aurata suka yi magana da jaririnsu da basu haifa ba. Hakan na bunkasa alakarsu. Kalmomi nada matukar girma kuma dole ne a fade su.

9. Kayi Saduwar Aure da ita don sanya jaririnta ya zama mai cikakkiyar lafiya.

Jima’i yayin da aka dauki ciki yana da matukar amfani ga matar da jaririn: yana taimakata tayi bacci mai dadi, yana saukaka hawan jini kuma yana sanyata farin ciki.

10.Ka shafe lokaci mai yawa kuna ibada tare.

Duk dangin dake ibada tare kuma su zauna tare suna girbar alkhairi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here