Duk Abinda Na Samu Zan Kashewa Al’ummar Nasarawa – Aranposu

0
296

Da Farko zamu so muji sunanka?

Sunana Auwal Shu’abu wanda aka fi sani da Aranpasu, tsohon mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano karo biyu a kan ICT.

Prime Time News: Kasancewar yanzu ka samu damar zama Chairman na karamar hukumar Nasarawa, kafin a kai ga wannan mataki, taya kaji sha’awar kana son zama shugaban karamar hukumar Nasarawa, me yaja hankalinka?

 

Toh farko dai zan ce dama da mai girma gwamna ya bani na nayi wannan aiki tare da shi a matsayi na mataimaki na musamman yasa na gano cewa ita harka ta shiga gwamnati ko ta siyasa, harka ce wacce zaka samu dama ka taimaki mutane, ka taimaki al’ummarka kuma ka taimaki wurin da ka fito. To sai nake ganin a mataimaki na musamman nake iya samun wannan dama kuma mutane sukan yaba kuma na kan ji dadi idan mutane sun yaba da an taimake su. Sai nake ganin wannan dama ce da yasa nima nayi sha’awar ina ganin idan na samu shugabanci ko wata kujera a matsayin zababbe zan fi taimakon al’umma fiye da yadda nake yi a matsayin mataimaki na musamman wanda wannan kaga nadi ne. Wannan shi ne ya bani sha’awa na shiga wannan takara kuma Allah ya tabbatar na zama shugaban karamar hukumar Nasarawa.

Prime Time News: Akwai Yan takarkaru da dama da suka fito daga wannan karamar hukuma kuma a karshe dai kai ne ka samu wannan dama ta yin takara, shin tayaya aka yi har ka iya doke wadannan ragowar yan takara??

Mun fito dayawa, masu neman wannan kujera a karamar hukumar Nasarawa kuma dama duk sanda aka fito takara kowacce iri ce, mutane sukan fito sa yawa amma Allah ya riga ya hukunta mutum daya ne zai kasance. Toh kuma a wannan kadami da muka samu kanmu ita jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce baza ayi zabuka ba sai dai za’aje ayi sulhu tsakanin yan takarkaru, toh duk wanda Allah yasa shi ne zai zama dantakara. Kuma muma a irin wannan yanayi muka samu kanmu, bayan anyi sulhun ma sai da aka yi wani abu wanda zance “Endorsement” shi ne muka samu mafi rinjaye na masu ruwa da tsaki da suke wannan tafiya tamu kusan kashi 70 ko 80 sun amince nayi takarar nan bayan haka mun samu delegates su kansu sun goyi bayana. Wannan duka anyi shi a rubuce kuma shi ne muka gabatarwa ita uwar jam’iyya ta jiha wannan shi ne ya bani dama na zama dan takara.

Prime Time News: Toh kafin samun wannan takara wane kalubale aka fuskanta tun lokacin da ka nuna sha’awa har kuma lokacin da Allah ya bada dama aka samu takara kafin a shiga zabe?

Toh! Kalubale da aka fuskanta..babu wani kalubale sai naje kalubale ne wanda har yanzu ana fuskantarshi wanda mutane basu yarda cewar shi duk mutumin da ya fito yin takara ba ko kuma ya fito ya shugabance su, yazo ne don ya bautawa al’umma ba, Aa mutane su kullum gani suke kawai in ka fito takara dole kazo kayi ta raba kudi ba wai nace duka mutane ba, amma an samu an samu wani kaso na mutane wadanda su wannan abun suke kallo har yanzu mutane basa kiraka suce “muna da kalubale kaza a yankinmu muna bukatar abu kaza a yankinmu”, Aa sai dai mutum yayi ta dakko matsaloli wadanda nashi ne na kashin kansa yayi ta fuskantarka da shi wanda yakamata ace shi yaje yayi maganin wannan abubuwan ya barka ka kalli ita karamar hukumar da kuma al’umma. Toh tun daga randa na fito takara zuwa yanzu wadannan su ne kalubalen da nake fuskanta amma amma ni a kullum duk sanda na samu dama zan yi magana da mutane na kan gayawa mutane cewar su gane bai kamata mutane su dinga fuskantar shugabanni da kalubale nasu na kashin kansu ba, su dinga fuskantar shugabanni da kalubale wanda na al’unma ne idan aka zo aka yi shi ko da kai baka samu ba zaka ga al’ummarka sun samu. Toh tunda na fito takara wannan kalubalen shi ne wanda na samu kuma har yanzu nake samun shi duk da wannan kalubale dake samu na kan yi iya kokarin a matsayina na rage wasu abubuwan.

Prime Time News: Akwai wani salo da ka fito da shi na lokacin yakin neman zabe na ” Siyasa dai-dai da Zamani” mai wannan yake nufi?

 

Siyasa dai-dai da zamani kusan ni al’ada ce girmama manya, girmama dai-dai dani, girmama kannena da kuma mutunta kowa kuma abinda yasa nazo da wannan Siyasa dai-dai da zamani, shi ne wannan siyasa zamu zo muyi ne da kowa da kowa baza mu ware wasu nau’i na mutane, muce baza muyi mu’ammala dasu ba matasa, mata, yara, iyaye da kowa da kowa zamu tafi dashi kuma idan ka kula da yanayin siyasa zaka ga har yan jam’iyyun adawa sun zo sunyi tafiya tare da mu ka’in da na’in wannan shi ne siyasa dai-dai da zamani muna so mu tafi da kowa da kowa abinda muke so mutane su gane shi ne ci gaba muka zo da shi, ci gaban al’umma shi ne agabanmu, yaza ayi a taimaki al’umma shi ne a gabanmu wannan shi ne Siyasa dai-dai da zamani kuma mutane sun karbi wannan abun suna yi.

Prime Time News: Toh bayan an kammala zabe yanzu za’a fara aiki, shin mai al’ummar karamar hukumar Nasarawa za su fuskanta daga gareka ?

Kamar yadda nake fada ko na sha fada a duk wuraren da na samu damar yin magana shi ne , mun riga munsan kalubale da Duniya Najeriya, Jihar Kano take fuskanta. Wanda mun ringa mun san cewa idan aka bar kananan hukumomi da kudin da ake turo musu, wasu kananan hukumomin ma baza su iya albashi ba. Toh wannan na riga nasan kalubale wanda ba ni ba duk wani shugaban karamar hukuma zai fuskance shi. Amma abinda na tabbatarwa da mutane shi ne duk wani abu da muka samu daga jiha ko tarayya da kuma abinda muka samu muka rora a kasa wato na Haraji zamu yi kokari mu yiwa al’ummar wannan karamar hukumar aiki, za mu duba kalubale wanda muke ganin zamu iya dai-dai aljihun karamar hukuma muyi shi. Wadannan su ne abubuwan da zamu yi kuma mutane su bamu hadin kai kuma su samu kwanciyar hankali da mun zo ne domin mu alkinta rayuwarsu, ba wani abu da muka zo muyi face mu kyautata musu Insha Allah duk wani abu da yazo daga karamar hukumar nan zamu tabbata mun kashe shi a karamar hukumar nan .

Prime Time News: Akwai zarge-zarge da aka dinga yi cewa, dan takarar karamar hukumar Nasarawa yaro ne bashi da shekaru, bashi da kwarewa ta siyasa kuma bai chan-chanta ya samu takara ba duk da cewa duk da cewa akwai manya-manya yan siyasa dake takarar amma ya samu dama me zaka ce game da wannan zargin?

 

Ni daman abinda na sani tun ina yaro shi ne indai kafito kace zaka yi takara ta siyasa kawai sai dai ka toshe kunnanka kayi takara, idan Allah ya tabbatar ma kayi abinda yake na dai-dai amma kada ka taba tunanin kowa da kowa zai goyi bayanka ko kuma zai zo da abu wanda zai karfafa ma gwiwa, duk lokacin da kafi takara mutane za’a nemi wani abu naka, wani gaske ne amma zaka ga kusan kashi 90 karya ne don kawai a karyama gwiwa ko ayima kage, idan mutum ya ce ni yaro ne bani da mu’ammala da mutane, toh a kalla nayi hulda da mutane kusan kananan hukumomi 44 ba iya karamar hukumar Nasarwa ba. Mukamin da na rike na aiki tare da mai girma gwamna bana jin akwai wani abu mara kyau ko na rashin mu’ammala tare dani haka shi yasa wannan mai girma gwamna ya yaba yadda mutane suka ji dadi kuma gwamnatin taji dadin yin mu’ammala dani yasa aka kara bani wannan mukami na kara dawowa a karo na biyu. Wanda muna daga cikin sahun farko da aka fara bawa wannan mukami kaga maganar ace bani da mu’amala wani abu ne daban. Inaga lokacin da mai girma mataimakin gwamna ya yi shugaban karamar hukumar Nasarawa ba mamaki muna shekaru daya. Kuma a yanzu idan kana magana ta rayuwa ina da mata biyu inda da yara toh kuma kazo kayi maganar cewa bani da mu’mala ko kuma yaro ne ni wannan duk abu ne na mutane wanda kuma baza ka hana su su fada ba sabida ba mamaki suna da wanda suke goyan ba kuma kaga zai yi kokarin kai abokin hanayyarsa kasa ko ta wane hali, amma ni surutu yawanci na Rediyo bai dameni ba don na riga nasan yawanci daukar nau’yinsu ake a kan basu kudi suje su fadi abinda ba shikkenan ba kuma mu a tsarin mu na Siyasa dai-dai da zamani, baza mu taba bawa wani kudi yaje gidan rediyo ya fadi abinda bashi muke yi ba ko yadi wani abu na bata wani .

 

Prime Time News: Ya alakarka da ragowar yan takarkaru wadanda suka nemi kujerrar shugabancin karamar hukumar Nasarawa.?

Toh kusan kashi 99 na yan takarkaru da muka yi takara dasu yan jam’iyya, ba wanda bai zo anyi wannan tafiyar dashi ba ya bada goyan bayansa kuma anyi mu’amala dashi ya goyin bayan tafiyarnan yayi mubaya’a, in takaice ma kusan tun kafin ace nine dan takara yawancinsu sunzo sun goyi bayana, alakata da dukkan yan takarkaru tana da kyau zance kuma zance kashi 100 muna da fahimtar juna.

Primes Time News: Akwai kalubale da kananan hukumomi suke fuskanta na rashin samun kudaden shiga daga kai tsaye sai yabi ta hannnun gwamnatin jiha wanda kuma wannan kalubale wanda tun lokacin da gwamnatin baya ta kirkiro wannan abu kananan hukumomi suka shiga halin ni’ya su , shin yaza ka fuskanci wannan kalubale?.

Toh wannan kamar na riga na fada abaya kalubale wanda ba wai iya jihar Kano bane ko iya jihohin Najeriya, kusan abu ne da ya shafi duniya na tattalin arziki, mai girma gwamna yana da niyya mai kyau kan kananan hukumomi yasan su ne suke kusa da jama’a, zan iya tunawa kusan ana gobe zabe mun zauna da mai girma gwamna ya tabbatar da insha Allah zai yi kokari yaga ya kirki wasu hanyoyi zai tabbatar da kananan hukumomi suna samun kulawa ta musamman, nasan insha Allah da irin wannan kulawa da zamu samu zamu kyautata yadda kananan hukumomi fiye da baya indai Allah yasa wannnan dama ta samu.

Prime Time News: A karshe wane kira zaka yi da mai girma gwamna kan kulawa da su kananan hukumomi da ka fara magana a yanzu?

Mai girma gwamna nasan a kodayaushe al’umma na kasa talakawa su ne a zuciyarshi yana da tausyi sosai kuma na san insha Allah mai girma gwamna zai yi duba da irin wannan yanayi da muka samu kanmu da kuma yanayi da al’umma suke ciki zai taimakawa kananan hukumomi zaj kyautata yadda suke tafiyar da yadda suke shugabanci a dukkan kananan hukumomi a jihar Kano ina da wannan tabbacin Insha Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here