Ƴan Shi’a Na Zanga-Zangar Adawa da Buhari a Kano

0
201

Daga Junaid Idris Gezawa

Daruruwan musulmai mabiya darikar Shi’a ne ke gudanar da zanga-zanga yanzu haka a Kano, inda suke nema a gaggauta sakin shugabansu, Ibrahim Elzakzaky.

Masu zanga-zangar dauke da takardu da rubuce-rubuce a jiki, sun yi jerin gwano a kan titin birnin Kano inda suke bayyana tsarewar da aka yiwa shugaban nasu a matsayin rashin adalci.

Wakilin jaridar SAHELIAN TIMES ya hango masu zanga-zangar a titin Sabon Titin Mandawari inda suka nufi hanyar gidan Sarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here