Yanzu-Yanzu: Za’ayiwa Buhari da Osinbajo Allurar Rigakafin Korona Ranar Asabar a Bainar Jama’a

0
65

Za’a iya shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo Allurar Rigakafin Korona ta AstraZeneca ranar Asabar.

Babban daraktan hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa, Dakta Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a Fadar shugaban kasa dake Abuja.

Acewarsa hakan zai kara kwarin gwiwa ga Yan Najeriya wajen karbar allurar rigakafin guda miliyan 4 da ta iso Najeriya a farkon makon nan.

Dakta Shuiab ya ce “mataki na gaba shi ne bayan yanzu mun karbi rigakafin sai kaddamar da shi wanda za’a yi a babban asibitin kasa gobe Juma’a da karfe goma na Safe. Shugaban kwamitin yaki da Korona ne zai kaddamar da rigakafin.

“Tsarin shi ne fara yiwa ma’aikatan lafiya rigakafin wadanda suke aiki a cibiyoyin kula da lafiya.

“Bayan haka, sai ayiwa shugaban kasa da mataimakinsa ranar Asabar da sauran shugabanni. Muna fatan idan yan Najeriya suka ga shugabanni kamar shugaban kasa da mataimakinsa anyi musu Allurar rigakafin; hakan zai karfafa gwiwarsu kan rigakafin”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here