Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 60 tare da Ƙone Garin Ruwan Tofa a Jihar Zamfara

0
239

Gungun yan bindiga sun kone wani kauye da ake kira Ruwan Tofa a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, tare da sace mutane 60, wadanda yawancinsu mata da kananan yara ne.

Yayin kai harin, yan bindigar sun tsere da kudaden mutanen garin, tare da harbe wani mara lafiya dake kwance a Asibiti kamar yadda jaridar SAHELIAN TIMES ta rawaito.

Hakan na zuwa ne kwanaki 2 bayan gwamnati ta tattauna da yan bindiga wanda ya kai ga sakin dalibai sama da 200 na makarantar Jangebe a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here