Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 tare da Sace Mutum 1 a Kano

0
384

Yan Bindiga sun shiga garin Rurum a karamar hukumar Rano ta jihar Kano, da misalin karfe 1 na dare ranar Talata inda suka sace mahaifiyar wani Dan Kasuwa mai suna Alhaji Yusuf Jibril.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa, yan bindigar sun bude wuta, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutane uku tare sace Alhaji Yusuf Jibril da matarsa, Hajiya Asabe Jibril sai dai daga bisani sun saki mijin.

Ya kuma ce an harbi dan’uwansa wanda daga baya ya rasu a ranar Laraba a asibitin Malam Aminu Kano, yayin da ragowar mutanen da suka hada da wani dattijo da suka kubuta daga hannun yan bindigar suke karbar magani.

Ya kara da cewa, jami’an tsaro basu isa wajen ba har sai dai yan bindigar suka gama aikinsu. Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce yan bindigar sun sace mutane biyu amma sun kubutar da daya kuma suna kan hanyar kubutar da dayan.

Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan sabon kwamishinan yan sanda ya fara aiki a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here