Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar Kano ta Karbi Bakuncin takwararta ta jihar Katsina

0
86

Darakta Janar na Hukumar Samar da Magunguna ta jihar Kano, Pharmacist Hisham Imamu Deen, ya karbi bakuncin tawaga daga takwarar hukumar reshen jihar Katsina.

Daraktan ya shaidawa tawagar irin kokarin gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano wajen samar da hanyoyin inganta lafiyar al’ummar jihar Kano.

Sannan ya yi bayanin nasarar da aka samu wajen dakile yaduwar annobar Korona da goyan bayan da gwamnan Kano ke badawa wajen tabbatar da kula da lafiyar al’umma.

Tawagar hukumar ta jihar Katsina tazo Kano ne don neman sani kan yadda Kano ke bin tsarin tafikar da ayyukan hukumar.

Tawagar ma’aikatan hukumar samar da magunguna ta jihar Kano ce dai ta karbi tawagar ta jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here