Hukumar Kula da Ilimin Bai daya ta Jihar Kano za ta Horar da Malaman Makaranta don Inganta Koyarwa a Makarantu

0
185

Shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano(SUBEB), Dakta Danlami Hayyo, ya ce hukumar za ta ci gaba da hadin gwiwa da kungiyoyin dake da ruwa da tsaki wajen bada horo ga malaman makaranta don kara bunkasa gogewar wasu wajen koyarwa.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da aka aikowa jaridar PRIME TIMW NEWS a jiya Talata wacce ke dauke da sa hannun Daraktan hulda da jama’a na hukumar, Balarabe Danlami Jazuli.

Dakta Hayyo ya bada da tabbacin ne yayin da yake jawabi ga malaman makaranta yayin taron bada horo da UBEC da hadin gwiwa da hukumar SUBEB suka shirya a dakin taro na hukumar.

Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin Alhaji Baffa Saleh, Sakataren hukumar ya ce gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta na bada muhimmanci ga fannin ilimi ta hanyar gina sabbin ajujuwa, samar da kayayyakin aiki, bada horo ga malamai da kula da walwalarsu.

Ya ce, an bada horon ne don kara azama ga malaman makarantu da jajirtattun ma’aikatan SUBEB wajen koyarwa a makarantun Firamare inda ya kara da cewa an zabi malamai 2625 da ma’aikatan hukumar 50 daga kananan hukumomi 44 na jihar don basu horon na kwana 3 kan dabarun koyarwa.

Yayin da yake godewa gwamnatin Kano bisa goyan baya da take bawa hukumar, shugaban hukumar ya bukaci wadanda suka halarci horon da su yi amfani da abinda suka koya wajen nuna shi ga dalibai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here